Tiriliyan kusan ukku aka kashe a bana a ragin kudin mai, duk da Buhari ya cire tallafin

Tiriliyan kusan ukku aka kashe a bana a ragin kudin mai, duk da Buhari ya cire tallafin

- Gwamnatin tarraya ta kashe 2.6trn akan shigowa da man fetur

- Ta kashe wannan kudade ne a cikin watanni tara

- Idan aka hada da shekara ta 2017 an samu karin kashi 67%

Kasafin kudin 2019: Majalisar Wakilai ta bada bayyana kudirinta kan ziyarar Buhari
Kasafin kudin 2019: Majalisar Wakilai ta bada bayyana kudirinta kan ziyarar Buhari
Asali: Twitter

Najeriya ta kashe kudi 2.582Trn akan shigowa da man fetur a cikin watanni Tara na shekara ta 2018.

Adadin da kasar ta kashe akan shigowa da man fetur a cikin watanni Tara yakai 28.3 daga cikin budget din 9.12trn da kasar ta fitar na shekara ta 2018.

NNPC ce ta bayyana hakan inda tace gwamnatin tarayya ta biya masu aikin man N236b

Ma'aikatan hukumar ta dillancin man fetur DAPPMAN sun tabbatar da biyan nasu da akayi.

A bangaren hukumar kididdiga NBS tace a cikin watanni Ukun karshe na shekarar kudin da Najeriya ta kashe akan shigowa da man yakai N845.12b da kuma N720.4b a farko da tsakiyar shekarar.

DUBA WANNAN: Tsage gaskiya: Aikin waye kawo jirgin kasa daga Abuja zuwa jihohi?

A cikin bayanin wata wata akan shigowa da man daga watan Junairu, Febrairu, March, Afrilu, Mayu da kuma Yuni kasar ta kashe N384.59b, N357.45b, N103.08b, N190.26b, N380.7b da kuma N149.44b.

Yayin da a cikin watan Yuli, Agusta da Satumba kasar ta kashe N343.25b, N378b, N295.03b.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa.

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel