Anyi kira ga Atiku Abubakar da ya rage kudin cefane kada ya kashe duka a kamfe

Anyi kira ga Atiku Abubakar da ya rage kudin cefane kada ya kashe duka a kamfe

- Gwamnan jihar Kaduna ya bayyana ra'ayin shi akan takarar shugabancin kasar nan

- Duk wanda yayi takara da Buhari yana batawa kansa lokaci ne

- Shawarar da zan bawa Atiku shine karya kashe duk kudin shi.cewar El rufai

Anyi kira ga Atiku Abubakar da ya rage kudin cefane kada ya kashe duka a kamfe

Anyi kira ga Atiku Abubakar da ya rage kudin cefane kada ya kashe duka a kamfe
Source: Facebook

Gwamnan jihar Kaduna Naseer El-rufai ya bayyana nashi ra'ayin akan 'yan takarar shugabancin kasar nan a badi 2019.

Gwamnan yace duk wani dan takara da yake karawa da Muhammad Buhari to fa yakai kansa halaka ne a siyasance don kuwa ba samu zaiyi ba.

Gwamnan na jihar Kaduna, ya shawarci dan takarar shugabancin kasar na jam'iyyar PDP wato Atiku Abubakar da karya kashe dukkanin kudin sa dan kuwa zai bukaci na cefane bayan zabe.

El-rufai ya kara da cewa shi abinda ya fahimta ya kuma yadda dashi shine cewa babu wani dan takara da zai goga da Buhari.

Duk kuma wanda yace zaiyi to fa yana cikin matsala dan kuwa yana batawa kansa lokaci ne.

DUBA WANNAN: Sojin Najeriya sun dagawa UNICEF kafa, bayan zargin leken asiri da ake musu a

Wannan dai shine karo na hudu da Atiku Abubakar ke neman shugabancin kasar nan, ya nema a PDP, sannan ACN, sai a PDP, sai APC, sannan ya dawo PDP.

Yanzu yana da shekaru akalla 70 a duniya, kuma shi ya kawo su El-Rufai da Nuhu Ribadu gwamnati a 1999.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa.

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel