Masu gudun hijira 250,000 ne suka koma gidajensu a jihohin tsakiyar Najeriya a bana

Masu gudun hijira 250,000 ne suka koma gidajensu a jihohin tsakiyar Najeriya a bana

- Yan gudun hijira 236,864 ne suka koma gidajen su a garuruwan su

- Manjo Janar Adeyemi Yekini ya jagoranci yan jarida zuwa kauyukan da ta'addancin ya shafa

- Kauyukan da abun ya shafa sun hada ta Mbabai, Mbadwen, Umenge, Yogbo duk a karamar hukumar Guma, Keana da Giza a jihar Nasarawa

Masu gudun hijira 250,000 ne suka koma gidajensu a jihohin tsakiyar Najeriya a bana

Masu gudun hijira 250,000 ne suka koma gidajensu a jihohin tsakiyar Najeriya a bana
Source: Facebook

Tashar labarai ta Daily Nigerian, ta ruwaito cewa shugaban 'Operation whirl stroke' shine yake kula da jihohin Benue, Nasarawa da Taraba.

Yayi bayanin yanda cikin 236,854 yan gudun hijira suka koma gidajen su. 201,854 daga jihar Benue, 15,000 daga Nasarawa sai kuma 10,000 daga jihar Taraba.

Kamar yadda yace, 141,000 na yan gudun hijirar na daga karamar hukumar Guma, 33,000 daga Gwer ta yamma sai 27,000 daga karamar hukumar Logo.

Yace OPWS tare da Operation 777 sun samu sama da manyan makami 20, makamai daruruwa, sun kama tare da mika sama da yan ta'adda 100 tare da gurgunta kungiyoyin yan ta'addan dake fadin jihohin uku.

Manjo Janar din ya sake tabbatar da maida hankalin OPWS wanda yace don komawa lafiyar yan gudun hijirar zuwa gidajen su ne tare da tabbatar da cewa duk wani ta'addancin dake faruwa a jihohin sun wanko shi.

Chief Abugh Air, mai unguwar Mbadwen ya jinjiinawa Gwamnatin tarayyar Najeriya akan kokarin da tayi wajen tabbatar da komawar yan gudun hijirar gidajen su.

DUBA WANNAN: An baiwa Atiku shawara kan rayuwa bayan zabe

Mista Ajir yace suna morar dadin zaman lafiya domin wasu daga cikin komammun har sun fara girbe kayan gonar su.

Yayi kira ga Gwamnatin tarayya da ta kara gina musu gadojin da rikicin ya kawo Lalacewar su don tabbatar da yan gudun hijirar sun dawo gidajen su da kuma inganta tsaro a yankin.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa.

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel