Tattalin arziki: Access Bank ta karbe Diamond Bank

Tattalin arziki: Access Bank ta karbe Diamond Bank

A farkon makon nan ne mu ka samu labari cewa bankin nan na Access Bank ya kamalla sayen Diamond Bank Plc. Bankin na Diamond ya tabbatar da wannan yarjejeniya ga Duniya a Ranar Litinin dinnan.

Tattalin arziki: Access Bank ta karbe Diamond Bank
Diamond Bank ya hada kai da Access Bank a Najeriya
Asali: Depositphotos

A kokarin da babban bankin Najeriya ke yi na karfafa bankunan Kasar nan, an saida bankin Diamond Bank zuwa ga Access Bank inda yanzu su ka zama su ke da mallakae bankin. Hakan dai zai karawa duka bankunan karfi.

Bankin Access wanda yana da karfi kwarai ne ya karbi ragamar Diamond Bank din. Shekarun baya, Access Bank ta saye Intercontinental BankPLC, ko da dai wannan ciniki da aka yi ya zo da sarkakiya har aka kori Ma’aikata.

KU KARANTA: Jami’an Gwamnati su na damfarar ‘Yan kasuwa a tsarin TraderMoni

A kwanakin baya ne babban Jami’in Diamond Bank Plc., Uzoma Dozie ya bayyana cewa za su daina aiki a kasashen ketare domin su maida hankali a Najeriya. Bankin yayi haka ne saboda karancin jari da yake ta fama da shi.

Dama can bankin ya saida kadarorin sa da sauran mallakar sa da ke kasashen waje irin su Kasar Ingila da kuma nan gida Afrika. A watan jiya ne dai abubuwa su ka sake tabarbarewa bankin ainun har ta kai aka dauki wannan mataki

Bayan wannan hadin kai da aka samu tsakanin Diamond Bank da kuma Access Bank, bankunan za su kara karfi inda za su zama bankin da ya fi kowane banki a Yankin Afrika yawan jama'a inji Masana harkar tattalin arziki a Kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng