Zidane zai nemi ya maye gurbin Jose Mourinho a Manchester – Laurens

Zidane zai nemi ya maye gurbin Jose Mourinho a Manchester – Laurens

Dazu nan ne Kungiyar Manchester United ta sanar da cewa ta sallami Jose Mourinho daga aikin horas da ‘Yan kwallon ta. Yanzu haka rahotanni sun ce Zinedine Zidane yana nuna sha’awar jan ragamar kungiyar.

Zidane zai nemi ya maye gurbin Jose Mourinho a Manchester – Laurens
Zinedine Zidane na iya karbar aikin Man Utd inji Express Sport
Asali: Getty Images

Duk da cewa dillalin tsohon Kocin na Real Madrid, Alain Migliaccioya bayyana cewa Zidane bai da shirin aiki a Kasar Ingila, akwai yiwuwar Manchester United ya ba tsohon ‘Dan kwallon sha’awa ganin an fatattaki Jose Mourinho.

Tun ba yau ba ake kiran cewa Zidane zai maye gurbin Jose Mourinho ganin yadda Kungiyar ta gaza tabuka wani abin a yaba. Wani Masanin harkar kwallon kafa mai suna Julien Laurens yace Zidane na iya dawowa Ingila da wasa.

KU KARANTA: Zidane ya gindayawa Man Utd sharudan komawa Ingila

Laurens yace Zidane zai yi sha’awar aiki a babban Kulob irin Manchster United, Fitaccen Masanin harkar kwallon kafan yace Kocin ya iya rike kulob cikin zaman lafiya kamar yadda yayi aiki a Madrid na tsawon shekaru biyu da rabi.

Laurens yake ganin cewa idan har Zidane ya rike Kungiyar Manchester United, kowane ‘Dan wasa zai ji cewa ana yi da shi a Kulob din. A cewar su kuma zai yi wahala wani kulob ya dauki Mourinho aiki bayan an gane irin halin sa a Duniya.

Julien Laurens ya fadawa wani gidan Jarida cewa da wuya Manchester United ba ta dauko hayar Zidane ba, sannan kuma a karshe yace dole sai dai Jose Mourinho ya koma gida ya horas da Kungiyar kwallon kafa na kasar sa ta Portugal.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel