Tsage gaskiya: Aikin waye kawo jirgin kasa daga Abuja zuwa jihohi?

Tsage gaskiya: Aikin waye kawo jirgin kasa daga Abuja zuwa jihohi?

- A bana ne Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da masu bada umarni da injinan jiragen kasan Abuja zuwa Kaduna

- Shugaban ya hau jirgi daga Rigasa zuwa Kakuri na jihar Kaduna

- Sanata Bruce yace shugaba Buhari yayi godiya ga tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan

Watanni shida da muka dauka kafin kafa gwamnati, laifin Jonathan ne, gwamnatin APC
Watanni shida da muka dauka kafin kafa gwamnati, laifin Jonathan ne, gwamnatin APC
Asali: Depositphotos

A baba ne dai shugaban kasa Muhammadu Buhari ya je jihar Kaduna don kaddamar da sababbin masu bada umarni da injinan jiragen kasa na jiragen Abuja zuwa Kaduna. Kuma jam'iyyar APC tace ita tayi wannan aiki.

Bayan kaddamarwar ne Shugaban ya hau jirgin kasan daga yankin Rigasa zuwa na Kakuri dake garin Kaduna. Sai dai jam'iyyar PDp tace runto ne aka yi mata na aiki.

Sanata Murray Bruce, Sanata mai wakiltar jihar Bayelsa ta gabas yace shugaba Buhari yayi godiya ga tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan da ya samar da damar hawa jirgin.

Bruce yace aiyukan jiragen kasan kacokan na daga cikin aiyukan Jonathan.

Amma Nasir El-Rufai, gwamnan jihar Kaduna, ya bawa Bruce amsa, cewa Gwamnatin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo wacce babu Jonathan kwata kwata a cikin ta ita ta fara aikin tare da samar da kudaden da aka yi aikin dasu.

Amma Bruce ya tsaya tsayin daka ta hanyar kalubalantar El-Rufai a bainar jama'a da ya fito suyi muhawara akan maganar.

Toh yanzu aikin jiragen kasa na Abuja zuwa Kaduna, na waye?

DUBA WANNAN: Sojin Najeriya sun dagawa UNICEF kafa, bayan zargin leken asiri da ake musu a baya

A watan Augusta 2017, makamancin hakan ya taso akan wanda ya amince da yin titunan jiragen kasa daga Kano zuwa Daura da karamar Hukumar Jibia dake jihar Katsina.

Kamar yadda titunan jiragen kasa na Daura zuwa Jibia, Kano zuwa Legas, haka shima Abuja zuwa Kaduna ba sabon aiki bane. Yana daga cikin tsarin da Jonathan yayi, wanda Buhari ya tabbatar da kammaluwar aikin.

A kashin gaskiya dai, tun Obasanjo aka faro wadannan ayyuka na jirgin kasa, kuma suna babbar takardar ci-gaban kasa da ake kira Master-Plan.

Suma kamfunnan CCECC dake qere-qeren, sun tabbatar a lokacin GEJ ne aka basu maqudan kudaden da suka iyar da wadannan ayyuka, su kuwa su shugaba Buhari, su suka kaddamar, suka kuma karasa ginin tashoshin da ma fadada ayyukan zuwa wasu jihohin.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel