Aiyukan da gwamnatin Buhari ke yi a jihohin arewa maso yamma

Aiyukan da gwamnatin Buhari ke yi a jihohin arewa maso yamma

An dade ana cece-kuce kan cewar tunda shugaba Buhari ya mulki ya mance da yankin da yafi yi masa ruwan kuri'u a zaben shekarar 2015. Sai dai hadiman gwamnatin Buhari sun sha musanta wannan zargi tare da bayyana cewar babu wata jihar da gwamnatin Buhari bata gudanar da aiki.

Domin kare kanta daga wannan zargi, gwamnatin tarayya ta fitar da jerin aiyukan da take yi a kowacce jiha.

Ga na yankin arewa maso yamma

1. Jigawa: Gyara da facin ramuka a hanyoyin Garki zuwa Gumel da Malam Madori zuwa Hadejia.

2. Kaduna: Ginin gidan wuta da zai samar da megawat 215 a Kudenda. Gyaran hanyar Ilorin-Jebba-Mokwa-Birnin Gwari da kuma toshe ramuka a hanyar Zaria zuwa Pambegua.

3. Katsina: cibiyar magance kwararowan hamada ta garin Daura da gina hanyoyin cikin garin.

Gyaran hanyar Katsina zuwa Batsari zuwa Safana.

Ginin gona ta musamman a Katsina (Katsina wind farm).

Aiyukan da gwamnatin Buhari ke yi a jihohin arewa maso yamma
Fashola; Ministan aiyuka, Gidaje da Lantarki
Asali: Depositphotos

4. Kebbi: Gyare-gyare a hanyar Kalgo-Bunza-Kamba-Peka.

5. Kano: Gina babbar hanyar Kano zuwa Maiduguri da gyaran hanyar Kano zuwa Zaria.

Gina wa da gyaran hanyar Saminaka zuwa Doguwa.

Ginin titin jirgin kasa daga Kano zuwa Kaduna da kuma wanda ya taso daga Legas zuwa Kano.

Ginin gidan yari a Janguza da kuma gyaran hanyar Kwanar Dumawa zuwa Babura ta jihar Jigawa.

DUBA WANNAN: Buhari zai mika mulki ga dan kabilar Igbo a 2023 - Sakataren gwamnatin tarayya

6. Sokoto: Gyaran hanyar Sokoto zuwa Tambuwal da zata hade da Jega zuwa Kontagora/Makera da kuma gyaran hanyar Kajiji zuwa Jabo a jihar Zamfara.

7. Zamfara: Toshe ramuka da gyaran hanyar Gusau zuwa Talata Marafa a jihar Sokoto.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel