Za a warware rikicin APC a Zamfara, in ji sanata Marafa bayan ganawa da Buhari

Za a warware rikicin APC a Zamfara, in ji sanata Marafa bayan ganawa da Buhari

Ciyaman din kwamitin majalisar dattawa na man fetur, Sanata Kabiru Garba Marafa (APC, Zamfara) ya ce ana gab da kawo karshen rikice-rikicen da ke jam'iyyar APC reshen jihar Zamfara bayan ganawar da ya yi da shugaba Muhammadu Buhari.

Jam'iyyar APC reshen jihar Zamfara ta gaza cika wa'addin da hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta bayar da mika sunayen 'yan takara gwamna, 'yan majalisun tarayya da na jihar a zaben 2019 sakamakon rikicin da aka rika yi wajen zaben fidda gwani.

A hirar da ya yi da manema labarai a karshen makon da ya gabata, Marafa ya ce ya gana da shugaban kasar ne domin tattaunawa a kan jinkirin da aka samu na biyan hakokin wasu dilalan man fetur, samar da tsaro a Zamfara da kuma rikita-rikatar da ke jam'iyyar APC na jihar.

Za a warware rikicin APC a Zamfara, in ji sanata Marafa bayan ganawa da Buhari

Za a warware rikicin APC a Zamfara, in ji sanata Marafa bayan ganawa da Buhari
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: A karon farko tun bayan faduwar PDP, Adamu Mu'azu ya shigo Najeriya

"Na gana da shugaban kasa saboda dalilai biyu, Na farko shine batun biyan kudaden dilalan man fetur wadda kwamitin da nake jagoranci ke kula da shi. An samu wasu matsaloli da ya shafi wadda idan ba a warware su ba wasu makiya gwamnati za su janyo mana layi a gidajen mai.

"Abu na biyu kuma shine halin da jam'iyyar APC ke ciki a jiha ta, Zamfara. Na zo domin in karu da shawarwari da kwarewar shugaban kasa wajen wareware matsaloli. Mun tattauna kuma ya bani shawarwari masu amfani kan yadda za a bullo wa lamarin," inji shi.

Da ya ke amsa tambaya a kan cewa ko an warware batun haramtawa jihar Zamfara gabatar da 'yan takara da INEC tayi, ya ce: "A'a, har yanzu muna kokarin warware matsalar. Lamarin yana kotu kuma muna sa ran nan da wasu makonni kadan za a samu mafita. "Mun san dukkan abinda ya faru saboda haka ba dai-dai bane a tattauna batun a jaridu tunda yana gaban kotu. Kamar yada na ce, muna gab da warware matsalolin," inji Marafa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel