Za a fafata wajen neman Gwamna a Jihar Kaduna a zaben 2019

Za a fafata wajen neman Gwamna a Jihar Kaduna a zaben 2019

Bisa dukkan alamu dai, a zaben badi na 2019, za ayi babbar karawa a Jihar Kaduna musamman tsakanin manyan Jam’iyyun Najeriya. Wadannan Jam’iyyu su ne; APC, PDP da kuma Jam’iyyar SDP da PRP.

Za a fafata wajen neman Gwamna a Jihar Kaduna a zaben 2019
Gwamna El-Rufai zai yi takara da Mace a Jihar Kaduna a zaben 2019
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust tayi nazarin yadda zaben na 2019 zai kaya. Jam’iyyu 36 ne za su fafata a zaben, amma kusan 4 ne su ka fi karfi. Mun kawo kadan daga cikin dogon sharhin da Jaridar tayi a kan ‘Yan takarar.

1. Nasir El-Rufai

Yanzu haka Gwamna mai-ci Malam Nasir El-Rufai, yana neman komawa kan karagar mulki a Jam’iyyar APC da gaske. Mutanen Kaduna su na kukan sallamar jama’a daga aikin yi duk da irin kokarin da yake yi a kan kujerar Gwamnan Jihar.

KU KARANTA: Abin kunya ne Atiku da Buhari su rika fada saboda kujera inji Wani Malami

2. Isa Ashiru Kudan

Babban mai kokarin takawa Gwamna mai-ci burki shi ne, Isa Ashiru Kudan wanda shi ne ‘Dan takarar Jam’iyyar hamayya ta PDP. Kudan rikakken ‘Dan siyasa ne, sai dai ba a jin sa yana yawon yakin neman zabe kamar ‘Dan takarar APC.

3. Haruna Sa’eed

Haruna Sa’eed ya nemi Gwamna a CPC a 2011, sai dai daga baya ya fice daga APC bayan ya koka cewa ba a damawa da shi. Kajuru ne zai yi takara a karkashin SPD wannan karo a Kaduna. Sai dai ana tunani zai yi fama da rashin kudi a Jam’iyyar.

4. Ahmed Umar

Tsohuwar Jam’iyyar nan ta PRP za ta buga da sauran Jam’iyyu a 2019 a Jihar Kaduna. Kwanan nan ne Jam’iyyar ta cire Alhaji Falalu Bello a matsayin ‘Dan takarar ta inda ta maye gurbin sa da Ahmed Umar. Umar zai jarraba farin jinin sa a 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel