'Yan ta'adda cikin kayan 'yan agaji sun kashe soja guda

'Yan ta'adda cikin kayan 'yan agaji sun kashe soja guda

Soja guda daya ya mutu yayin da dakarun soji suka dakile wani hari da mayakan kungiyar Boko Haram cikin kayan 'yan agaji suka kai masu a jihar Borno.

A sanarwar da mataimakin darektan hulda da jama'a na rundunar soji ta Ofireshon Lafiya Dole, Kanal Onyema Nwachukwu, ya fitar ya bayyana cewar mayakan kungiyar Boko Haram din sun yi yunkurin shiga wani wani kauye bayan sun yi basaja cikin kayan 'yan agaji.

Nwachukwu ya Kara da cewar mayakan sun fake ne da rabon kayan agaji da ake yi a garin tare da bude wuta a kan tawagar soji dake wurin.

'Yan ta'adda cikin kayan 'yan agaji sun kashe soja guda

'Yan ta'adda cikin kayan 'yan agaji sun kashe soja guda
Source: Depositphotos

Ya ce wasu gungun mayakan dake kan wata mota mai dauke da bindiga sun cigaba da harbi bayan dakarun soji sun mayar da martani.

Nwachukwu ya ce, "rundunar soji ta Ofireshon Lafiya Dole dake sa ido kan rabon kayan agaji a Gudumbali sun dakile wani hari da mayakan kungiyar Boko Haram suka kawo bayan sun yi basaja cikin kayan 'yan agaji.

DUBA WANNAN: An kashe mutane 4 a wurin kaddamar da kamfen din Ganduje a Kano

"An yi musayar wuta tsakanin 'yan ta'addar da jami'an soji kuma an kashe da dama daga cikinsu.

"Sai dai abin takaici, saya daga cikin jami'an soji ya rasa ransa, wani guda a samu rauni yayin musayar wutar, sannan motar mu ta yaki guda ta lalace. "

Nwachukwu ya ce dakarun soji sun taho da gawarwakin mayakan da suka kashe tare da wasu makamansu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel