An kashe mutane 4 a wurin kaddamar da kamfen din Ganduje a Kano

An kashe mutane 4 a wurin kaddamar da kamfen din Ganduje a Kano

Rahotanni sun bayyana cewar mutane 4 sun mutu ciki mako guda a yayin da gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya kaddamar da yakin neman zabensa a kananan hukumomin Bichi da Rano.

Gwamna Ganduje ne dan takarar jam'iyyar APC a jihar Kano duk da fama da zargin karbar rashawa da yake fama da shi.

Ya kaddamar da yakin neman zabensa ranar Lahadin makon jiya, 9 ga watan Disamba, a karamar hukumar Bichi inda aka bayyana cewar mutum guda ya mutu sakamakon rikici tsakanin magoya bayan gwamnan da masu adawa da shi.

An kashe mutane 4 a wurin kaddamar da kamfen din Ganduje a Kano

Ganduje
Source: Depositphotos

A yayin taron, gwamna Ganduje ya raba tutar jam'iyyar ga 'yan takarar kujeru daban-daban dake sanatoriyar Kano ta arewa.

DUBA WANNAN: Yadda karuwai da 'yan fashi suka hana Sanata Lawan zama shugaban majalisar dattijai - Tinubu

Aminu Fagge, abokin siyasar mutumin da aka kashe, ya ce sunan marigayin Sarki Yunusa, kwararren mafarauci dan asalin karamar hukumar Minjibir.

A ranar Asabar, 15 ga watan Disamba, Ganduje ya kara jagorantar kaddamar da wani kamfen din a karamar hukumar Rano. Rahotanni sun bayyana cewar mutane uku ne aka kashe yayin taron. Karamar hukumar Rano, dake sanatoriyar Kano ta Kudu, na daga cikin kananan hukumomin Kano da jam'iyyar APC keda karfi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel