Hadimul Islama ya tasamma karas da kaba'ira a birnin Kano da kewaye

Hadimul Islama ya tasamma karas da kaba'ira a birnin Kano da kewaye

- Kano dai shari'ar Islama take, wadda ta haramta al-hamru

- Sai dai Najeriya ba kan sharia'a take ba, kuma ta baiwa kowa damar yaje inda yake so

- Hisba na son lalata duk wata giya da aka kawo jiharta

Hadimul Islama ya tasamma karas da kaba'ira a birnin Kano da kewaye

Hadimul Islama ya tasamma karas da kaba'ira a birnin Kano da kewaye
Source: Depositphotos

Ana dab da zabukan 2019, Hisba a Kano ta tasamma kawar da masha'a da kaba'ira, domin ta farantawa mazauna jihar rai, koda kuwa hakan zai bakantawa wasu, musamman baki daga jihohin kudu da ma ma'aikata daga kasashen waje.

Hukumar ta sha alwashin lalata duk wata kwalbar giya da aka kawo jihar, koda kuwa ba musulmi ne ke sha ba.

A yanzu hukumar, tace kwalabe miliyan daya zata lalata kafin bukukuwan kirsimeti, biki na addinai da ke bukatar wanna ruwan giya domin su farantawa kansu.

DUBA WANNAN: A karon farko Janar IBB ya dawo bayan shugaba Buhari kan batun tsaro, yayi masa jinjina

Jihar Kano dai, akwai maguzawa, akwai musulmi, kirista, 'yan Indiya da ma na China masu zuwa kasuwanci, kuma suna rayuwa da juna lafiya, abin lura kuma su suke qere-qere a jihar, inda su wadanda ke son ayi shari'ar, iyakarsu saye ko sayarwa.

Akwai masana'atu a jihar Kano, amma duk na mutane ne da suka zo suka zuba jari, su kuwa Kanawa, suna daukar kudinsu ne su gina Islamiyya da Masallatai.

Mr. Nahabani Usman, shugaban tsare-tsare na hukumar Hisba da doka ta baiwa dama, yace sun kama kwalaben na giya ne a kokarin jama'ar jihar na holewa lokacin bukukuwan kirsimeti, ya kuma ce duk wasu muggan kwayoyi sun haramta a jihar.

A gefe daya kuma yayi kira ga masu iyawa, masu kudi, dasu kara aure, domin a kara wa al'ummar annabi yawa a jihar, a kuma kawar da yawan zawarawa da suka fi na ko'ina yawa a duniya.

An dai haramta karuwanci a Kano, sai dai masu neman lalata sun koma wa kananan yara, inda hukumomi ke karbar koke-koken fyade dubbai a kowanne wata.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa.

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel