Cika baki: Babu tababa Shugaba Buhari zai zarce a 2019 - Gwamna Lalong

Cika baki: Babu tababa Shugaba Buhari zai zarce a 2019 - Gwamna Lalong

- Gwamnan Filato yayi alkawarin taya Shugaba Buhari yakin zabe a 2019

- Simon Lalong yace babu shakka cewa Buhari zai zarce kan mukamin sa

- Lalong da mukarraban sa sun nuna cewa sai inda karfin su ya kare a badi

Cika baki: Babu tababa Shugaba Buhari zai zarce a 2019 - Gwamna Lalong

Gwamna Lalong da kwamishinonin sa za su taya Buhari yakin zaben 2019
Source: Depositphotos

Mun samu labari daga Jaridar Daily Trust ta Kasar nan cewa Gwamnan Jihar Filato, Mai Girma Simon Bako Lalong ya bayyana cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ci zaben 2019 ya gama a Jam’iyyar APC mai mulki.

Gwamna Simon Lalong yayi wannan jawabi ne a cikin karshen makon nan a lokacin da ya kaddamar da ofishin yakin neman zaben sa na 2019. Jama’a da dama sun fito wajen taron yakin neman zaben Jam’iyyar APC a 2019.

KU KARANTA: Najeriya ta kere kowace Kasa wajen yara marasa zuwa karatu a Duniya

Ganin cincirindon al’umma ya sa Gwamnan yake ganin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari kamar ya koma kan kujerar sa ne a 2019. Lalong yacae Mutanen Filato su na tare da Jam’iyyar APC a zaben da za ayi a shekarar badi.

Gwamnan da ke kokarin zarcewa kan kujerar sa ya bayyana cewa yanzu lokaci kurum ake jira a sake rantsar da Shugaba Buhari a karo na biyu. Gwamnan yace a shirya yake da jama’an sa su yi wa Buhari yaki a babban zaben 2019.

Gwamna Lalong yace Gwamnonin adawa na PDP sun yabawa kokarin da Buhari yayi na farfado da sha’anin tsaro a Najeriya. A Ranar Juma’a ne Shugaba Buhari ya gana da duka Gwamnonin Najeriya a fadar Shugaban kasa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel