Shehu Sani ya fadi abinda Buhari ya yi da babu shugaba a duniya da ya taba yi

Shehu Sani ya fadi abinda Buhari ya yi da babu shugaba a duniya da ya taba yi

Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattijai, sanata Shehu Sani, ya yi jinjina ga shugaban kasa, Muhammadu Buhari, bisa fadin gaskiyar halin da tattalin arzikin Najeriya ke ciki a yayin da ake daf da gudanar da zabukan shekarar 2019.

Shehu Sani ya bayyana cewar shugaba Buhari ya yi namijin kokari wajen fadin gaskiya ba tare da la'akari da cewar yana yin takara a zaben 2019 ba, Sanatan ya ce babu wani shugaba a duniya da zai iya yin wannan abu da Buhari ya yi.

Sanatan ya yi wadannan kalamai ne a cikin wasu sakonni da ya wallafa a shafinsa na Tuwita a yau, Asabar.

A cewar Shehu Sani, "shugaba Buhari ya cancanci jinjina bisa fadin gaskiyar halin da tattalin arzikin Najeriya ke ciki a lokacin da ya rage kwanaki kadan a yi zaben 2019. Da yawa zasu yi karya domin samun kuri'u.

"Ban san wani shugaban kasa a tarihin duniya da ya taba irin wannan kalami yayin da ya rage kwanaki kadan a yi zabe ba," a cewar Shehu Sani.

Shehu Sani ya fadi abinda Buhari ya yi da babu shugaba a duniya da ya taba yi
Buhari da Shehu Sani
Asali: Depositphotos

A jiya, Juma'a, ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gargadi gwamnoni da ragowar shugabanni a kan su kara kulla damara domin fuskantar tsananin da ya fi na baya saboda halin da tattalin arzikin kasa ke ciki.

DUBA WANNAN: Gagararrun 'yan fashi sun fada komar 'yan sanda a Katsina, hotuna

Shugaba Buhari ya yi wannan kalami ne yayin ganawar sa ta sirri da gwamnonin kasar nan jiya a Abuja.

Gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari, ne ya bayyana hakan ga manema labarai bayan kammala ganawar su da shugaba Buhari.

A cewar gwamnan, shugaba Buhari ya sanar da su cewar tattalin arzikin Najeriya na cikin mawuyacin hali, tare da kalubalantar su a kan bullo da hanyoyin da za a inganta tattalin arzikin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel