Faduwa jarrabawa: Hameed Ali zai yi kora a hukumar kwastam
Shugaban hukumar kwastam ta kasa (NCS), Hameed Ali, ya ce zai kori dukkan jami'in kwastam da ya fadi jarrabawar kwalejin hukumar sau uku.
Shugaban na wannan kalami ne a wurin bikin yaye manya da kananan jami'an hukumar kwastam da suka kammala karatu a kwalejin kwastam ta Abuja a jiya, Juma'a.
Ya bayyana cewar yin hakan na daga cikin sabbin dokokin hukumar kwastam na inganta aiyukan jami'anta.
Kazalika ya bayyana cewar halartar kwalejin horon ya zama dole ga kowanne jami'in hukumar daga yanzu.
"Lokacin yiwa jami'an hukumar kwastam karin girma saboda sun ci kashi 99.9% a jarrabawa ya wuce, daga yanzu zamu ke yin karin girma ne ka jami'an da suka nuna kwazo.
"Idan ka halarci kwalejin horo sau uku ba tare da ci jarrabawa ba, to karshen aikinka a hukumar kwastam ya zo.
"Muna aiki tukuru don ganin mun karfafa wannan doka tare da tabbatar da cewar kowanne jami'in kwastam ya halarci kwalejin horo da ta dace da mukaminsa.
DUBA WANNAN: 2019: Jami'ar Cambridge ta kasar Ingila ta gayyaci 'yan takarar shugaban kasa 5
"Daga yanzu, karin girma zuwa mukami na gaba da kuma tura jami'ai zuwa wuraren sabbin aiki zai dogara ne da kwazon mutum a kwalejin horo. Kuma daga yanzu halartar kwalejin horo ya zama dole ga dukkan jami'an hukumar kwastam ko wadanda aka zaba," a kalaman Hameed Ali.
Daga karshe, ya shaidawa jami'an hukumar ta kwastam cewar zasu fara amfani da sabuwar dokar domin nuna muhimmanci da amfaninta.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng