A gaskiya PDP na sanya ma'aikatanmu cikin hadari - INEC ta koka

A gaskiya PDP na sanya ma'aikatanmu cikin hadari - INEC ta koka

- A lokacin da yakin neman zaben ya tsananta ne ake zargin INEC da zata yi magudin zabe

- INEC tace wannan kalaman kiyayyar zasu iya jefa ma'aikatan ta a hatsari

- PDP tace fadar shugaban kasa ta umarci INEC da ta kirkiro sababbin wuraren kada kuri'u don magudin zabe

A gaskiya PDP na sanya ma'aikatanmu cikin hadari - INEC ta koka
A gaskiya PDP na sanya ma'aikatanmu cikin hadari - INEC ta koka
Asali: Twitter

A lokacin da yakin neman zaben shekara mai zuwa ya tsananta, babbar jam'iyyar siyasar kasar da hukumar zabe mai zaman kanta ke ta fuskantar zargin burin yin magudin zabe daga babbar jam'iyyar adawa ta PDP.

Jam'iyyar PDP tace yunkurin kirkirar gurin zabe a sansanin yan gudun hijira yunkurin APC ne da INEC don yin magudin zabe.

Farfesa Mahmood Yakubu, shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa a take ya fatattaki zargin ta hanyar Kwatanta shi da kalamin kiyayya wanda zai iya jefa ma'aikatan hukumar a wani hali yayin zabe mai zuwa.

Jam'iyyar dake mulki, tace yan Najeriya sun gaji kuma sun gudura da iyayyakun da kullum PDP ke bullo da ita tare da kalubalantar jam'iyyar da su sanar da yan Najeriya dalilin da zai sa su kara zabar su don mulkar su.

DUBA WANNAN: Sabon garambawul da za'a yiwa matatun man kasar nan bayan tazarce

Sakataren hulda da jama'a na kasa na jam'iyyar PDP, Mista Kola Ologbondiyan, a taron manema labarai yace duk sansanin yan gudun hijira dake kasar nan sun fada ne karkashin gurin yin zabe.

Kamar yanda yace, "Saboda jaddadawa, PDP bata amince da wata sigar damfara ba ta hanyar yin shirye shirye na musamman don yin magudin zabe. Jam'iyyar mu tana kara jaddada cewa ayi zabe a wuraren yin zabe kadai na fadin kasar nan. PDP da ma duk yan Najeriya basu shirya karba sakamakon da za'a kirkira ba daga wasu wuraren zabe don taimakon shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi magudin zabe.

Jam'iyyar PDP ta zargi fadar shugaban kasa ta umartar INEC da ta bude sababbin wuraren kada kuri'u a hamada da kuma gabar Chadi da Nijar don amfani dasu wajen magudin zaben shugaban kasa a 2019.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa.

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel