Sojoji sun ragargaji 'yan ta'addar Zamfara, hotunan wadanda suka mutu
Dakarun Sojin Najeriya na 8 Division da ke aikin samar da zaman lafiya na Sharan Daji sunyi nasarar kashe wasu 'yan ta'adda da suka dade suna adabar mazauna karamar hukumar tsafe a jihar Zamfara.
Kamar yadda bayanin sirri na soji ya nuna, an yiwa 'yan ta'addar kwantar bauna ne Tungar Rakumi a ranar 12 ga watan Disamba. Bayan artabu da 'yan bindigar, soji sun kashe 'yan bindiga 2 sannan sun kwato bindigu AK 47 guda biyu da harsasai masu yawa.
Kazalika, dakarun soji na Sector 3 da ke aiki da 'yan aikin sa kai na Civilian sun damke wani gawurtaccen dilalin bindigu mai suna Lawali Aliyu a hanyar zuwa kauyen Araba da ke karamar hukumar Illela a jihar Sokoto a ranar 13 ga watan Disambar 2018.
An damke shi dauke da bindigu da makamai a cikin buhu. An kwace makaman kuma an tsia keyarsa zuwa ofishin yan sandan Najeriya da ke Sokoto domin cigaba da bincike.
Ga hotunnan a kasa.
DUBA WANNAN: Kwanan nan ta'addanci a Zamfara zai zama tarihi - Buratai ya ci al washi
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng