Ya kamata a soke tsarin Shugaban kasa da Mataimakin sa – Inji ‘Yan Majalisa

Ya kamata a soke tsarin Shugaban kasa da Mataimakin sa – Inji ‘Yan Majalisa

Wasu gungun ‘Yan Majalisar Tarayyan Najeriya sun soma kira a canza tsarin shugabancin Kasar a koma yadda aka fara tun farko a tarihin kasar. ‘Yan Majalisar sun yi wannan kira ne a zaman da aka yi jiya.

Ya kamata soke tsarin Shugaban kasa da Mataimakin sa – Inji ‘Yan Majalisa
Majalisa na so a daina amfani da tsarin Shugaban kasa da Mataimaki
Asali: UGC

‘Yan Majalisar Wakilan Najeriya har 71 ne su ke neman a sake salon shugabancin da ake yi a Kasar nan zuwa tsarin shugabanci na Firayim Minista. Mafi yawan ‘Yan Majalisar da su ke wannan kira sun fito ne dga Jam’iyyar adawa ta PDP.

Honarabul Kingsley Chinda wanda ke wakiltar Yankin Ribas da kuma wani Takwaran sa daga Jihar Delta, Nicholas Ossai sun zanta da manema labarai bayan sun gabatar da wannan kudirin a gaban Majalisar Tarayyar a jiya Alhamis.

‘Yan Majalisar su ka ce irin tsarin shugabanci na Firayim Minista ya fi saukin sha’ani da kuma saukin kashe kudi don haka su ke kira a koma irin wancan salo na Gwamnati, ayi watsi da tsarin da ake kai a yanzu a Najeriya domin a huta.

KU KARANTA: Buhari ya samu goyon baya a zaben 2019 daga wasu Taurarin Najeriya

‘Yan Majalisar su ka ce irin wannan salo na mulki ta hanyar Shugaban kasa da Mataimakin sa bai kari Najeriya da komai ba illa talauci. ‘Yan Majalisun su ka nuna cewa bincike ya tabbatar tsarin Firayim Minista ya fi kawo cigaba a Duniya.

Daga cikin ‘Yan Majalisar da ke goyon bayan wannan kudiri akwai Abdulsamad Dasuki, Boma Goodhead, Timothy Golu, Gabriel Onyenwife, Sergius Ogun, da Emeka Ujam. Idan an amince da kudirin, za a mikawa Shugaban kasa ya sa hannu.

Najeriya dai ta soma aiki ne da irin tsarin mulkin Firayim Minista bayan 1954 kafin Sojoji su hambarar da Gwamnatin Kasar a farkon 1966. A dawowar 1979 ne aka koma soma aiki da wannan tsari na Shugaban Kasa da Mataimakin sa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel