Waiwaye cikin 2018: Manyan al'amura 6 da suka girgiza Najeriya

Waiwaye cikin 2018: Manyan al'amura 6 da suka girgiza Najeriya

Shekarar 2018 ta tasanma karewa kuma 'yan Najeriya sun fara shirin tarbar sabuwar shekarar 2019. Hakan yasa muka ga ya dace ayi bita a kan wasu muhimman abubuwan da suka faru a shekarar ta 2018.

Wasu abubuwan da suka faru na farin ciki ne yayin da wasu kuma na bakin ciki ne da ban mamaki da sauransu.

Legit.ng ta tattaro muku wasu muhimman abubuwan da suka faru a shekarar ta 2018 a yanzu da muke shirin shuga sabuwar shekarar da mutane da yawa ke fatan abubuwan alkhairi za su faru.

1. Gobarar gadan Otedola

A ranar 28 ga watan Yunin 2018, a kalla mutane 9 ne suka kone kurmusu yayin da motocci 54 suka kone sakamakon gobarar da wata tanka dauke da man fetur tayi a gadan Otedola. Gobarar ya faru ne a kusa da tsohuwar Toll gate da ke Alausa a Legas.

2. Bacewar Janar Alkali a jihar Plateau

Hukumar Sojin Najeriya ta sanar da bacewar jami'inta, Janar Idirs Alkali a ranar 3 ga watan Disamba a hanyarsa ta zuwa Bauchi daga Abuja.

Daga bisani an gano motarsa, takalmansa da kayansa a wani kududufi da ke Dura Du a jihar Plateau inda bincike ya kai ga kama wasu mutane takwas da ake zargi da hannu cikin kashe shi.

Daga baya an gano gawarsa cikin wata tsohuwar rijiya a ranar 31 ga watan Oktoba a kauyen Guchwet a Shen da ke karamar hukumar Jos ta kudu na jihar Plateau kuma daga baya anyi jana'izarsa a Abuja.

DUBA WANNAN: Sojoji sun ragargaji 'yan ta'addar Zamfara, hotunan wadanda suka mutu

3. Kisar kiyashi da Boko Haram suka yiwa sojojin Najeriya a Metele

A ranar 24 ga watan Nuwamba, labarain harin da Boko Haram suka kai a sasanin sojin Najeriya ta tayar da hankalin masu bibiyar kafafen sada zumunta.

A yayin da wasu rahotanni suka ce kimanin sojoji 100 suka mutu a harin, amma sanarwar da hafsin hafsoshin Najeriya, Laftanat Janar, Tukur Buratai, ya fitar ya ce sojoji 23 ne aka kashe a harin na Metele.

A cewar Buratai, sojoji 39 aka kashe yayin da wasu 43 suka jikkata. Buratai ya kuma ce an kai hari sansanin sojoji da ke Kukawa, Ngoshe, Kareto da Gajiram a tsakanin ranar 2 zuwa 17 ga watan Disamba.

4. Rugujewar gini a Portharcourt

Wani abin bakin ciki ya afku a daren Juma'a 23 ga watan Nuwaba inda wani gini mai bene bakwai ya ruguje a Woji GRA phase two a garin Portharcourt.

An tattaro cewa a kalla ma'aikata 200 da ke aikin ginin ne ginin ya fado musu.

Legit.ng ta tattaro cewa an ceto mutane 11 da ginin ya rufe, an kuma ce mutane biyar sun rasu.

5. Bayanar Nnamdi Kanu a kasar Isra'ila

Bayan bacewarsa yayin da sojin Najeriya suka kai sumame a gidan mahaifinsa, shugaban kungiyar masu fafutikan kafa Biyafra, IPOB ya sake bayyana a wani faifan bidiyo a watan Oktoba a kasar Isra'ila.

Bidiyon da ya bazu a kafafen sada zumunta ya nuna shugaban na IPOB yana Ibada a kasar Isra'ila.

Bayan fitowar bidiyon, shugaban MASSOB, Ralph Uwazurike ya umurci al'ummar Igbo suyi watsi da kirar da Kanu ya yi na cewa kada suyi zabe a shekarar 2019.

6. Saka hannu kan dokar rage shekarun shiga takara da Buhari ya yi

A ranar 31 ga watan Mayu, 'yan Najeriya da yawa sunyi murna bayan shugaba Muhammadu Buhari ya amince da dokar Not Too Young to Run wadda ya bawa matasa damar shiga takara domin a dama da su.

Sai dai cikin ba'a, shugaba Buhari ya yi kira da matasa su hakura da neman takarar shugabancin kasa sai bayan shekarar 2019.

Shugaban kasar ya taya matasa murna kuma ya bukaci suyi amfani da damar da suka samu domin zama masu dogaro da kansu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel