Kwanan nan ta'addanci a Zamfara zai zama tarihi - Buratai ya ci al washi

Kwanan nan ta'addanci a Zamfara zai zama tarihi - Buratai ya ci al washi

- An mayar da rundunar sojin 1 Briget daga jihar Sokoto zuwa birnin Gusau da ke jihar Zamfara

- An dauki wannan mataki ne domin karfafa matakan tsaro da kawo karshen ta'addanci da kashe-kashe a Zamfara

- Gwamnatin jihar Zamfara ta bawa rundunar ta 1 Briget gudunmawar sabuwar katafaren sansani a Gusau

Shugaban hafsin sojojin kasa na Najeriya, Laftanat Janar Tukur Buratai ya ce kashe-kashe da sauran ta'addanci da ke adabar jihar Zamfara ya kusa zuwa karshe.

Mr Buratai ya yi wannan furucin ne a ranar Alhamis a Gusau yayin kaddamar ta tambarin Shaho da tambarin sojin Najeriya yayin bikin karbar sabuwar katafaren sansanin soji da gwamnatin jihar Zamfara ta bawa sojin Najeriya.

An kusa kawo karshe ta'addancin 'yan bindiga - Buratai
An kusa kawo karshe ta'addancin 'yan bindiga - Buratai
Asali: Depositphotos

Shugaban sojin wanda ya samu wakilcin kwamandan Sojin Kasa, Hakeem Otiki ya yabawa gwamnatin jihar Zamfara saboda tallafa wa sojin da sansanin tare da cewa sojojin ba za suyi kasa a gwiwa ba wajen kiyaye kasar.

DUBA WANNAN: Laifi ne saduwa a cikin mota - Hukumar 'yan sanda ta karyata jami'inta

Ya ce za a bawa 1 Birget da ke Zamfara dukkan kayayakin aiki da sojoji da suke bukata domin magance barazanar tsaro da ake fama da shi a jihar.

Ya yi kira da dakarun sojin su cigaba da goyon bayan demokradiyya da ake yi a kasar kuma su dena nuna fifiko ga kowanne dan siyasa.

Buratai ya ce tambarin Shaho na Briget din yana nufin zaman lafiya, jarumtaka da karfi.

A baya, Kwamandan Birigade din, Lynus Udeagbala ya ce matsao da brigade din daga Sokoto zuwa Gusau da koma gudunmawar ginin da gwamnatin jihar Zamfara ta bawa sojin zai saukaka ayyukansu kuma za su dage wajen bawa marada kunya.

Ya ce dakarun sojin sabuwar sansanin za su rika hadin gwiwa da sauran hukumomin tsaro domin ganin an magance barazanar ta'addanci da ma wasu laifuka a jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel