Kotu ta daure wasu kananan barayi da EFCC ta kamo, bayan sunyi damfarar N12m

Kotu ta daure wasu kananan barayi da EFCC ta kamo, bayan sunyi damfarar N12m

- Kotu ta wulla wasu yara kurkuku

- Sunyi damfarar N12.5m ne

- Babu sani babu sabo kan harkar kudi

Kotu ta daure wasu kananan barayi da EFCC ta kamo, bayan sunyi damfarar N12m
Kotu ta daure wasu kananan barayi da EFCC ta kamo, bayan sunyi damfarar N12m
Asali: Facebook

Abin tausayi da takaici baya qarewa, inda a yau hukumar EFCC ta saki hotunan wasu kananun yara da alkalai a kotu suka samu da laifin zamba cikin aminci, kuma suka daure su a kotu, zaman watanni, babu kuma uzurin kankanta ko tara.

Kotu ta daure wasu kananan barayi da EFCC ta kamo, bayan sunyi damfarar N12m
Kotu ta daure wasu kananan barayi da EFCC ta kamo, bayan sunyi damfarar N12m
Asali: Facebook

Oluwalusi Kikelomo da mukarrabanta a jihar Edo, an same su da laifin zamba cikin aminci gaban kotun birnin Benin, inda alkali Justice M. G. Umar ya same su da laifin da ya taka doka.

Kotu ta daure wasu kananan barayi da EFCC ta kamo, bayan sunyi damfarar N12m
Kotu ta daure wasu kananan barayi da EFCC ta kamo, bayan sunyi damfarar N12m
Asali: Facebook

Bata dai musa cewa ta aikata zambar ba, wanda hakan ya sa ta sami sassaukan hukunci, na watanni shida a kurkuku, da aiki, je gyara hali.

An kuma amshe dukkan kaya da kadarori da ta saya da kudin, an damqa wa wadda suka zambata, dukkan wannan ya faru ne a yau alhamis a babban birnin na Edo.

DUBA WANNAN: Najeriya zata samar da wutar lantarki har 20,000 MegaWatt cikin shekaru biyu - TCN

Laiin da aka same ta dashi dai, shine, bayann an dauke ta aiki a O- FAGE Enterprise Nigeria Ltd, tun daga watan February na 2017, take sata a ofishin tana sayar da kadarorin, kuma tana sayen abinda take so. Jimillar kudin ta kai hae N12,200,000.

Ezean Chukwuebukai Lawrence kuma, an same shi da laifin N168,000.00 da ya kwashe daga bankin wata Okosun Christiana, ta hanyar zamba.

Sai kuma Magbo Chukwujekwu Hillary. shima N160,000 ya cinye wa ita dai Christina din. Dukkaninsu sun sami zaman kaso na watanni bi-biyu, kuma an kwace abubuwan da suka saya an mayar wa da mai qara.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa.

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel