Najeriya zata samar da wutar lantarki har 20,000 MegaWatt cikin shekaru biyu - TCN

Najeriya zata samar da wutar lantarki har 20,000 MegaWatt cikin shekaru biyu - TCN

- Kamfanin tura wutar lantarki na kokarin rarrabawa megawatts 20,000 nan da 2021

- TCN ta saka sama da Megawatts 3000 daga watan Fabrairu zuwa yanzu

- Ana kokarin kara samarwa, rarrabawa da tura wutar lantarki

Najeriya zata samar da wutar lantarki har 20,000 MegaWatt cikin shekaru biyu - TCN
Najeriya zata samar da wutar lantarki har 20,000 MegaWatt cikin shekaru biyu - TCN
Asali: Depositphotos

Kamfanin tura wutar lantarki ta Najeriya, TCN na kokarin cimma tura megawatts 20,000 nan da 2021, inji manajan Darakta, Usman Mohammed.

Mista Mohammed ya sanar da manema labarai a ranar litinin a fadar shugaban kasa cewa yawan tura lantarkin aikin tiransifomomi da layika.

DUBA WANNAN: Kamfanin Lantarkin Kaduna Electric, ya kaiwa Sarkin Zazzau ziyarar aiki

Kamar yadda ya fada, TCN ta tura karin sama megawatt 3000 tun daga watan Fabrairu da ya hau kujerar shi.

A yanzu dai, kasar nan na lilo ne tsakanin MegaWatt 3,500 zuwa 7,000MW, lamari da gwamnati ke cewa ba laiinta bane, abin a hannun 'yan kasuwa yake.

Ya kuma ce ana kokarin fadada aiyukan samarwa, rarrabawa da tura wutar lantarki. Kamar yanda yace, akwai wuya tura wutar Idan aka danganta ta da rarrabawa.

Manajan Darakta yace da yawa daga cikin abubuwan da ake bukata na rarrabawa wuta ana hada su ne a Najeriya amma babu injin tura wutar lantarki da ake samar dashi a Najeriya.

Matsalar lantarkin kasar nan dai tun kaka-da-kakanni, kuma duk alkawurran gwamnatoci, a jiya da yau, ya kasa warware ta.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa.

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel