Akwai matsala a gidan Sojin Najeriya – inji tsohon ‘Dan Sandan Turai

Akwai matsala a gidan Sojin Najeriya – inji tsohon ‘Dan Sandan Turai

Wani tsohon babban Jami’in ‘Yan Sanda na Kasar Birtaniya, Vince Onyekwelu yayi fashin baki game da sha’anin tsaron Najeriya inda yace akwai matsala a tsarin shugabancin da ake da shi a gidan Sojin Najeriya.

Akwai matsala a gidan Sojin Najeriya – inji tsohon ‘Dan Sandan Turai
Onyekwelu yace Sojoji ba za su iya gamawa da ‘Yan Boko Haram a badi ba
Asali: Facebook

Vince Onyekwelu, wanda yayi aiki a Kasar Ingila a baya yayi magana a gidan Talabijin na Channels TV kwanan nan. Tsohon Jami’in ‘Dan Sandan yace rikicin Boko Haram ya ki karewa ne saboda matsalar da ake samu daga gidan Sojin kasar.

Onyekwelu yace ana horas da Rundunar Sojojin Najeriya ne a boye ba tare da jama’a sun san abin da yake faruwa ba. Tsohon ‘Dan Sandan ya kuma bayyana cewa a cikin sirri ake yin duk wasu ayyuka a gidan Sojin Najeriya a halin yanzu.

KU KARANTA: Za a kafa ma'aikatar cigaban yankin kudu maso gabas a Najeriya

Mista Vince Onyekwelu yace ba ya tunanin za a kawo karshen Boko Haram kwanan nan saboda irin tsarin shugabancin Rundunar Sojojin Najeriya. Tsohon ‘Dan Sandan wajen yace da wuya a iya kawo karshen Boko Haram shekara mai zuwa.

Sai dai Rundunar Sojin Najeriya ta bakin Janar Sani Usman Kukasheka, ta karyata rade-radin cewa Sojojin Kasar ba su samun isasshen horo da kayan aiki a fagen daga yadda ya kamata. Janar Kukasheka ya maida martani a ne gidan Talabijin.

Yanzu dai ‘Yan Boko Haram sun jefa sama da mutum 100, 000 na Arewa maso Gabashin Najeriya mawuyacin hali inda kwanaki ku ka ji cewa ‘Yan Najeriya rututu da ke gudun hijira a Kasar Kamaru.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel