Rundunar Sojojin Najeriya sun kama yan ta’adda 3, sun kwace bindigu 44

Rundunar Sojojin Najeriya sun kama yan ta’adda 3, sun kwace bindigu 44

Rundunar Sojojin Najeriya ta sanar da kama wasu mutane guda uku da ake zargin yan ta’adda ne a jahar yayin da suke safarar bindigu zuwa kauyen Bena dake cikin karamar hukumar Wasagu ta jahar Kebbi, kauyen dake da iyaka da jahar Zamfara.

Majiyar Legit.com ta ruwaito mataimakin kaakakin rundunar ta daya na rundunar Sojin Najeriya, Kanal Muhammad Dole ne ya sanar da haka a ranar Laraba 12 ga watan Disamba, inda yace Sojoji sun kama yan ta’addan ne a ranar Talata 11 a yayin binciken ababen hawa a garin Rijau na jahar Neja.

KU KARANTA; Masu yi don Allah: Babban jami’in kwastam ya yi fatali da tayin cin hancin naira miliyan 50

Rundunar Sojojin Najeriya sun kama yan ta’adda 3, sun kwace bindigu 44
Bindigu
Asali: UGC

Kanal Dole ya bayyana sunayen yan ta’addan kamar haka; Aminu Umar dan shekara 32, Shehu Samaila dan shekara 25 da kuma Bilyaminu Abdullahi mai shekaru 22, inda ya kara da cewa sun kama yan ta’addan dauke da bindigu guda arba’in da hudu (44).

Haka zalika kaakakin yace sun kwato kwankunan alburusai guda dari uku da hamsin da daya, 351, duk a cikin motar da yan ta’addan suke ciki mai lamban rajista ZUR 28DX Kebbi, yayin da suke kan hanyarsu ta shiga jahar Kebbi.

“Bincikenmu ya binciko yan bindigan na kan hanyarsu ta zuwa kauyen Bena ne dake cikin karamar hukumar Wasagu na jahar Kebbi, wanda kuma yana da iyaka da jahar Zamfara.

"Wannan kamen da muka yi yazo daya da wani mutumi, Rabiu Akilu da muka kama dauke da bindigu 36 da alburusai 343 a cikin motarsa yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa Zamfara a watan Nuwamba.” Inji shi.

Daga karshe kanal Dole yace zasu cigaba da gudanar da bincike akan Aminu, Shehu da Bilyaminu domin jin wanda zasu kai ma makaman da kuma wanda ya basu makaman, don haka yayi kira ga direbobi dasu taimaka ma Sojoji da sahihan bayanai game da ayyukan yan bindiga.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel