Shugaba Buhari na godiya ga kasashen da suka dawo da kudin sata na Najeriya

Shugaba Buhari na godiya ga kasashen da suka dawo da kudin sata na Najeriya

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi wa kasar Swizalan godiyar dawo da kudaden da aka handame

- Dawowa da kudaden na nuna cewa Gwamnatin Swiss na son cigaban Najeriya

- Taimakon da Gwamnatin ta Switzerland don ke bada wa a arewa maso gabas ba kadan bane

Shugaba Buhari na godiya ga kasashen da suka dawo da kudin sata na Najeriya
Shugaba Buhari na godiya ga kasashen da suka dawo da kudin sata na Najeriya
Asali: Facebook

A yau talata a garin Abuja shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika godiyar Gwamnatin Najeriya ga Gwamnati da kuma yan kasar Swiss bisa taimakon farfado da tattalin arzikin Najeriya ta hanyar dawo da kudin da aka handame.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace dawo da kudaden da aka handame tare da tallafawa arewa maso gabas na nuna Gwamnatin Swiss na son cigaban Najeriya.

Shugaba Buhari na godiya ga kasashen da suka dawo da kudin sata na Najeriya
Shugaba Buhari na godiya ga kasashen da suka dawo da kudin sata na Najeriya
Asali: Twitter

"Muna godiya ga Gwamnatin Swiss sakamakon dawo da kudin da aka sara Najeriya," inji shi.

DUBA WANNAN: PDP ta riga ta fadi a 2019 - APC

Shugaban ya tabbatar da rawar da Gwamnatin Swiss ke takawa ga arewa maso gabas, ballantana 'yan gudun hijira na kara karfafa dankon aminci tsakanin kasashen biyu.

Jakadan Gwamnatin Swiss a Najeriya yace zasu cigaba da tallafawa Najeriya don tabbatar da zaman lafiya, ballantana a yankin arewa maso gabas.

Sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel