2019: Daya daga cikin manyan hadiman Kwankwasiyya ya koma Gandujiyya

2019: Daya daga cikin manyan hadiman Kwankwasiyya ya koma Gandujiyya

Tsohon kwamishinan Kwamishinan ayyuka na musamman a jihar Kano, Idris Dambazau ya raba jiha da jam'iyyar PDP ya koma APC. Ana kyautata zaton ficewar Dambazau ba zai rasa nasaba da zabin surukin Kwankwaso, Abba Yusuf a matsayin dan takarar gwamnan PDP a zaben 2019 ba.

Tsohon kwamishinan ayyuka na musamman a jihar Kano, Idris Dambazau ya shiga jam'iyyar All Progressives Congress, APC.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa Mr Dambazau wanda tsohon Janar din soja ne shine yayan ministan harkokin cikin gida na yanzu, Abdulrahman Dambazau.

2019: Daya daga cikin manyan hadiman Kwankwasiyya ya koma Gandujiyya
2019: Daya daga cikin manyan hadiman Kwankwasiyya ya koma Gandujiyya
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: 2019: Korafin babban sarki a arewa ya kai APC hannun DSS

Anyi gumurzu da tsohon Janar din wanda ya jagorancin kwamitin tsaro na Kwankwasiyya a watan Augustan 2015 saboda ya ki mayar da motocin gwamnati 3 bayan saukarsa daga kujerar kwamishina.

Majiyar Legit.ng ta gano cewa komawa Gandujiyya da Dambazau ya yi ba zai rasa nasaba da zabin surukin Kwankwaso, Abba Yusuf a matsayin dan takarar gwamna na PDP da jam'iyyar ta yi ba.

A wani taro da gwamna Ganduje da sauran shugabanin APC suka hallarta a ranar Litinin a Kano, tsohon kwamishinan ya zargi Mr Kwankwaso da kama karya, da jiji da kai tare da wofintar da nasarorin da Kwankwasiyya da samu a jihar Kano.

Mr Dambazau ya hallarci taron sanye da kan hulla ta Kwankwasiya amma daga baya ya mika ta ga gwamna Ganduje domin a cinna mata wuta wadda alama ce da ke nuna bashi ba Kwankwasiyya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel