Hira da IBB ya bayar ta wannan shekarar ga 'yan Jarida, kan yadda lamurra suke yanzu a kasar nan

Hira da IBB ya bayar ta wannan shekarar ga 'yan Jarida, kan yadda lamurra suke yanzu a kasar nan

- Dan siyasa ne a yanzu kuma yayi mulkin soja

- Ya bar manya manyan tarihi a lokacin mulkin soja da kuma siyasar Najeriya

- "Kowa ya gaji da mulkin soja"

Hira da IBB kan yadda lamurra suke yanzu a kasar nan

Hira da IBB kan yadda lamurra suke yanzu a kasar nan
Source: UGC

A ranar 24 ga watan Yuli ne ya karbi bakunci manema labarai inda ya amsa tambayoyi na kusan awanni uku. Tambaya daya ce yaki amsawa saboda yana tunanin zata gurbata alakar shi da shugaban kasa Muhammadu Buhari:

A wata ranar juma'a ne 13 ga watan Fabrairu na 1976 Janar Ibrahim Badamosi Babangida ya baiwa kasar mamaki.

Kanal Bukar Suka Dimka, abokinshi na kusa ya jagoranci juyin mulkin da ya girgiza Najeriya da Afirka ma. Dimka da gungun shi suka kashe shugaban kasar lokacin, Janar Murtala Ramat Mohammed.

Sun tsinkayi harabar gidan rediyo don sanar da juyin mulkin. Babangida ya isa gidan rediyon inda ya ja hankalin shi da ya hakura, tun daga nan Babangida ya zama babba a tarihin siyasar Najeriya.

DUBA WANNAN: Hakkin yara: Ina gwamnatoci ne, da har yanzu limamai ke sanya wa yara laqanin maita?

Yayi magana akan rayuwar shi ba tare da Maryam ba, matarshi ta shekaru 40 ,rayuwar shi a matsayin soja, rawar da ya taka a juyin mulki biyu da suka canza tarihin Najeriya. Sannan yayi bayani akan zaben 12 ga watan Yuni wanda babban dan kasuwa da MKO Abiola suka ci.

Tsohon shugaban kasa na mulkin sojan ya sanar da majiyar mu cewa sunja kunnen 'yan Najeriya kan abubuwa da dama amma suka ki saurare.

Babangida yace :"Nace mubi komai a hankali ta hanyar koyo. Duk inda muka kakare sai mu tsaya, mu canza sannan mu cigaba. Amma sai suka ki ji. Kowa baya son mulkin soja." Kan batun Juyin mulki da zaben 1993 kenan.

IBB dai yana jam'iyyar PDP ne, kuma su suka taba juyar da Buhari a kan mulki a 1985, kuma suka yi ta kutun kutun kar ya dawo mulki, inda amma a 2011 suka yi ta kokarin suga ya samu ci, domin an kasa gane abin da GEJ yake nufi da batun bam din da ya fashe a Eagle Square, inda yake kare 'yan Neja Delta, yake laqa wa wasu 'manyan Janar' laifin hakan.

Daga nan kuma, manyan Janar dinnan kaf, sun sake juya wa Muhammadu Buhari baya kan batu tazarcensa a 2019.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel