'Yan Najeriya miliyan 13.5 sukayi zaben shugaban kasa a shekara ta 2015 ba tare da katin zabe na PVC ba

'Yan Najeriya miliyan 13.5 sukayi zaben shugaban kasa a shekara ta 2015 ba tare da katin zabe na PVC ba

- 'Yan Najeriya miliyan 13.5 sukayi zaben shugaban kasa a shekara ta 2015 ba tare da katin zabe ba

- Mutane biyu ne dai suka gwabza a zaben Shugaban kasar na shekara ta 2015

- Mafi yawancin jam'iyun an kada musu kuri'a ba tare da katin zabe ba

Majalisar dinkin duniya tace kusan mutum miliyan daya ne basu samun agaji a Najeriya
Majalisar dinkin duniya tace kusan mutum miliyan daya ne basu samun agaji a Najeriya
Asali: Depositphotos

A kalla yan Najeriya miliyan 13.5 ne suka kada kuri'a a zaben Shugaban kasa na shekara ta 2015 ba tare da katin zabe ba.

Binciken ya nuna cewa shugaban kasa Muhammad Buhari dan takarar jam'iyar APC yaci zaben jihohi 9 a cikin 10 daga cikin jihohin da sukafi kada kuri'ar.

Mafi yawan jam'iyun an kada musu kuri'a ba tare da katin zabe ba.

DUBA WANNAN: Audugar Al'ada: Shin me matan arewa ke bukata daga al'umma da gwamnatoci?

Zaben shugaban kasar na shekara ta 2015 yana da jiga jigan yan takara Buhari da Goodluck Shugaban kasa na farko daya rasa damar komawa kan kujerar sa a Najeriya.

Daga cikin kuri'u 31,746,490 da aka kada guda 13,536,511 an kada su ne ba tare da katin zabe ba.

10,184,720 daga cikin wadannan kuri'u na Buhari ne yayin da 3,351,519 suka kasance na Goodluck ne.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel