Buhari ya taya Nuhu Ribadu samun lambar yabo

Buhari ya taya Nuhu Ribadu samun lambar yabo

- Shugaba Muhammadu Buhari ya taya tsohon shugaban EFCC, Nuhu Ribadu murnar samun lamban yabo na ACE saboda rawar ta ya taka wajen yaki da rashawa

- Shugaban kasar ya ce wannan alama ce da ke nuna duniya tayi na'am da jajircewar da Najeriya keyi wajen yaki da rashawa

- Shugaba Buhari ya kuma shawarci dukkan 'yan Najeriya da ke rike da mukaman gwamnati su dauki mulkin a matsayin amana

Shugaba Muhammadu Buhari ya mika sakon taya murna ga tsohon shugaban hukumar yaki da masu yiwa arzikin kasa ta'annati EFCC, Malam Nuhu Ribadu bisa samun lambar yabo na yaki da rashawa ta Life Achievement.

Buhari ya taya Nuhu Ribadu samun lambar yabo
Buhari ya taya Nuhu Ribadu samun lambar yabo
Asali: Twitter

A sakonsa na taya murnar, shugaba Buhari ya ce ba karamin karamci bane aka yiwa tsohon shugaban na EFCC duba da cewa yana daya daga cikin mutane 8 daga nahiyoyi 5 da aka baiwa lambar yabon mai daraja na Sheikh Tamin Bin Hamad Al Thani International Anti-Corruption Excellence (ACE).

DUBA WANNAN: 2019: Atiku ya fadi abinda gwamnatinsa ba za ta yarda da shi ba idan aka zabe shi

Ya ce jajircewa da bajinta da ya yi ne wajen yaki da rashawa ya sanya aka bashi lambar yabon.

A cewar shugaban kasar, "lambar yabon da aka bai wa Ribadu ya jadada kwazon mu wajen yaki da rashawa wadda yana daya daga cikin abubuwa uku da gwamnatinmu ta sanya a gaba. Hakan kuma ya nuna cewa duniya tayi na'am da kokarin mu na magance rashawa a kasarmu."

Buhari ya taya Nuhu Ribadu samun lambar yabo
Buhari ya taya Nuhu Ribadu samun lambar yabo
Asali: UGC

Ya yi kira shugabanin hukumar ta EFCC da sauran hukumomin da ke yaki da rashawa a Najeriya su cigaba da jajircewa wajen yaki da rashawa a kowanne fani na kasar.

Shugaban kasar kuma ya yi kira da 'yan Najeriya da ke rike da madafan iko suyi koyi da Malam Ribadu ta hanyar daukan mulki a matsayin amana.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel