Hakkin yara: Ina gwamnatoci ne, da har yanzu limamai ke sanya wa yara laqanin maita?

Hakkin yara: Ina gwamnatoci ne, da har yanzu limamai ke sanya wa yara laqanin maita?

- Coci na take wa yara hakki a matsayinsu na yara kanana

- Masallatai ma da makarantun allo basu bar yara ba

- Gwamnatoci da 'yan siyasa suna dauke kai saboda neman goyon bayan maluman a zabe

Hakkin yara: Ina gwamnatoci ne, da har yanzu limamai ke sanya wa yara laqanin maita?

Hakkin yara: Ina gwamnatoci ne, da har yanzu limamai ke sanya wa yara laqanin maita?
Source: UGC

Matsalolin nahiyar Afirka da yawa, amma akwai matsaloli da sun shantake hankali, kamar lamarin Almajirta da ya kai har anyi yakokin Maitatsine da Boko Haram, amma babu mai hankalin a ya haramta shi, shekaru kusan 40.

A kudu kuma, da yankunan tsakiyar Najeiya, matsalar ta maita ce, wai kawai a kalli yaro a ce wai yana da aljannu ko maita, saboda tsabar chamffi, jahilci da zalunci.

A dukkan kasashe masu hankali, babu wannan matsalar, saboda sun san babu aljannu, babu maita, bokaye maqaryata ne, kuma tsafi da asiri bassu ci, aiki kawai ake da kimiyya da ilimin Boko, ba surkulle da zamba da sunan addinai ba.

DUBAN WANNAN: Najeriya 2019: Abubuwa 19 da matasan Najeriya ke jira sabuwar gwamnati tayi musu, kowaye kuwa yaci zabe

Jihar Kuros Ribas, a yankin Neja Delta, tafi duk irin wannan matsala a Najeriya, musamman ma a yankunan karkara, kuma gwamnati bata iya tanka wa limaman cocin, wadanda suke gallazawa yaran da ma kulle su a kemp-kemp na killacewa.

Mata da maza, kananan yara ake warewa a dinka saka musu magungunan gargajiya da tsubbu, da ma bulala, wai don aljannun su bar jikinsu.

Tabbas dai babu aljannu, babu mayu, babu duk wadannan camfe-camfe na tsafi da asiri da suke ci, hauka da jahilci ne kawai da maqalewa tatsuniyoyi.

Wannan shi yasa kasashen turawa suka iya mulkar mu suka kuma sayar damu a matsayin bayi, aljannun namu da bokaye basu tsinana mana komai ba.

Ko a yanzu, ma, zaka ji mata na cewa boka wane ko malami wane ya iya harka da aljannu ko fatalwa, su kai masa kudi ya basu dalasimai, amma babu wani aljani da yaje ya yaki Boko Haram ko ya kashe mana Shekau! Lallai asiri da tsafi karya ne.

Gwamnatoci su san malamai na addinai basu da wani karfin tsinuwa, su kwatowa yara hakkinsu kawai, koda kuwa zasu rasa quri'u, yin daidai shine yasa kasashen waje suka fi mu iya tunani.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel