Bayan an hana shan kodin, maganin mahaukata matasan Kano suka koma sha - Rahoto

Bayan an hana shan kodin, maganin mahaukata matasan Kano suka koma sha - Rahoto

- Kashi 70 da suka hada da matasa da yara mazan jihar Kano na amfani da miyagun kwayoyi

- NDLEA tace ta kwace miyagun kwayoyi kusan ton 10 tsakanin watan Janairu zuwa Disamba

- Shaye shayen matasan na da nasaba da talauci da rashin rashin aikin yi

Bayan an hana shan kodin, maganin mahaaukata matasan Kano suka koma sha - Rahoto
Bayan an hana shan kodin, maganin mahaaukata matasan Kano suka koma sha - Rahoto
Asali: Depositphotos

Darakta Janar na cibiyar kula da magunguna da abinci, NAFDAC, Mojisola Adeyeye, ya bayyana cewa kashi 70 na matasa da yara maza na amfani da miyagun kwayoyi a jihar Kano.

A Kano, matar shugaban kasa, Aisha Buhari da Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi II a jiya sun nuna cewa al'ada da kara wayar da kan iyali shine jigon kawo karshen matsalar a kasar nan.

A yayin da Buhari tafi jaddada kashe tushen matsalar, Sarkin ya jaddada cewa daukan tsauraran matakai akan masu amfani da kwayoyin da masu siyarwa shine mafita.

DUBA WANNAN: Kwastam fa ta tara wa gwamnati kudin da bata taba gani a lalitarta ba daga hukuma daya

Adeyeye ya jajanta cewa yara mata da manyan mata a kano sun fada dumu dumu cikin harkar kwaya. Yayi kira da goyon baya daga iyali gurin tabbatar da al'adu da koyarwar addinai don gyara rayuwar yara.

NDLEA tace ta kwace miyagun kwayoyi kusan ton 10 daga watan Janairu zuwa Disamba na 2018.

Sanusi ya danganta shan kwayoyin a kano da talauci, rashin aikin yi, barin karatu da yawan mutane. Ya bukaci hukumomin da suka danganta dasu tsaurara tsaro domin hana shigo da miyagun kwayoyin cikin kasar.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel