Dalilin shugaba Buhari na kin sanya hannu kan dokar zaben 2019 na kara fitowa fili

Dalilin shugaba Buhari na kin sanya hannu kan dokar zaben 2019 na kara fitowa fili

- Ko meye dalilin shugaban kasa na kin sanya hannu akan takaddar zabe

- Buhari bai sanya tsare tsaren ECOWAS a dalilin daya hanashi rattaba hannu akan takaddar ba

- Wannan dai shine karo na Hudu da aka mika takaddar gabansa danya rattaba hannu

Dalilin shugaba Buhari na kin sanya hannu kan dokar zaben 2019 na kara fitowa fili
Dalilin shugaba Buhari na kin sanya hannu kan dokar zaben 2019 na kara fitowa fili
Asali: Depositphotos

Sanatan dake wakiltar jihar Delta Ovic Omo Agege yace tsare tsaren ECOWAS akan harkar shugabanci shiya hana Shugaban kasa Muhammad Buhari rattaba hannu akan takaddar zabe.

Ya bayyana hakan ne a yayin wata tattaunawa ta hanyar wayar tafi da gidan ka da yayi da kamfanin dillancin labarai na NAN a ranar Juma'a a Abuja.

Omo- Agege wanda yake goyan bayan shugaban kasar ya kara da cewa idan Shugaban ya rattaba hannu akan takaddar watanni Uku kafin zabe to fa ya sabawa tsare tsaren ECOWAS.

DUBA WANNAN: An sake kwato 'yan Najeriya 200 daga qangin Bauta a Hamadar Saharar Libya

An tsayar da ranar 16 ga watan Fabrairu 2019 a matsayin ranar da za'ayi zaben shugaban kasa dana yan majalisa,yayin da na gwamnoni zai biyo baya a ranar 2 ga watan Mayu shekara ta 2019.

Agege ya kara da cewa idan lokacin daya kamata Shugaban ya rattaba hannu yayi to fa babu makawa zai rattaba hannun.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel