Wata sabuwa: Tazurai zasu fara biyan harajin rashin yin aure da wuri
Matasa da tazurai sun ga ta kansu a kasar Afirka ta kudu inda aka sanya dokar biyan haraji ga duk wani matashi ko tazuru da bai yi aure ba a yankin Nkuthu dake Arewacin Kwazulu Natal na kasar, kamar yadda talabijin na Enca ta ruwaito.
Majiyar Legit.com ta ruwaito duk wani matashin yankin daya kai munzalin aure daga shekara 18 zuwa abinda yayi sama kuma bai yi auren ba zai biya harajin Randi hamsin(R50) da aka yi ma lakabi da harajin ‘Samari marasa aure’, kamar yadda hukuma ta tanadar.
KU KARANTA: Mutane 8 sun rigamu gidan gaskiya a wani rikicin kabilanci daya barke a jahar Neja
Wani matashi dan shekara 31 mai suna Thamsanka Zwande da bashi da mata dake zaune a kauyen Bulamehlo dake karkashin yankin da aka kaddamar da doka, ya tabbatar da dokar, amma yace tunda har yanzu bashi da aikin yi, sai dai babarsa ta biyasa masa harajin.
Matashi Thamsanka Zwande ya bayyana cewa an aika takardar sanarwar harajin ga duk wani matashin daya haura shekara 18 kuma bashi da aure. “Eh, lallai an aiko min da takardar. Ba ni da mace ko budurwa da take zama da ni. Don haka zan rika biyan Randi 50 duk shekara.” Inji shi.
Sai dai a wani kaulin kuma, iyaye ne zasu biya ma yayansu da suka cika sharadin biyan harajin amma basu da kudi ko aiki kamar yadda wani magidanci Busisiwe Mthembu ya tabbatar ma majiyarmu.
A cewar Busisiwe Mthembu, yana da yara samari guda uku wanda dukkaninsu sun kai munzalin aure amma basu da mata, amma tunda basu da aikin yi, nauyin biyan harajin ya koma kansa. “Dole ne su biya harajin, na fara biya ma babban dana, sauran biyu da zasu cika shekara 18 nan bada jimawa, sum azan fara biya musu.” Inji shi.
Sai dai babban basaraken yankin, Thathezakhe Ngobese yayi watsi da jita jitan da ake yadawa na cewa wia shi ke tursasa ma jama’a biyan wannan kudi don amfanin kansa da iyalansa, kamar yadda rahotanni suka ruwaito.
A cewar basaraken, ana karbar kudin ne don amfani dasu ta hanyar kulawa da masarautar yankin tare da ma’aikatanta, ba wai shi ake tara mawa ba, kuma ba tursasa ma jama’ansa yayi ba game da dokar.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng