Yaki da rashawa: Malam Nuhu Ribadu ya samu lambar yabo daga kasar Malaysia
Tsohon shugaban hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, kuma shugabanta na farko, Malam Nuhu Ribadu ya samu lambar yabo tare da wasu mutane bakwai a kasar Malaysia sakamakon kokarinsu a wajen yaki da rashawa.
An zabo mutanen da suka cancanci karramawar ne daga yankunan nahiyoyin Asiya, Afirka, Amurka, Oceania da kuma nahiyar Turai, inda aka karramasu a wani kayataccen biki daya gudana a birnin Putrajaya na kasar Malaysia.
KU KARANTA: Gwamnatin Buhari za ta kaddamar da fara aikin wasu manyan madatsan ruwa guda 7
Wannan bikin karramawa an gudanar da shi ne a ranar yaki da rashawa ta tunawa da Sheikh Tamim Bin Hammad Al Thani karo na uku, wanda yayi daidai da ranar yaki da rashawa ta Duniya. Kamar yadda mashirya taron suka bayyana.
Daga cikin wadanda aka karrama a taron sun hada da; Sarkin Watar Tamim Al Thani, shugaban kasar Malaysia Mahathir Mohamad, daraktan yaki na shan kwayoyi da miyagun laifuka na majalisar dinkin duniya Yury Fedatov da kuma babban lauyan kasar Qatar Ali Marri.
Majiyar Legit.com ta ruwaito mashirya taron suna bayyana cewa sai da aka tankade, aka rairaye sa’annan aka tantance zababbun mutanen da aka karrama, suka kara da cewa an shirya taron ne haskaka yaki da rashawa, tare da karrama mutanen da suka taka rawar gani a yaki da rashawa.
Kasashen da suka yi fice wajen yaki da rashawa a shekarar 2018 sun hada da Liberia, Australia, Ghana, Nigeria, Afirka ta kudu, Papua, Amurka da kuma kasar Mexico, inda aka baiwa kowacce kasa daga ciki kyautar lambar yabo.
Shi dai Nuhu Ribadu tsohon jami’in Dansanda ne, wanda tsohon shugaban kasa Olusegu Obasanjo ya nadashi shugaban hukumar EFCC saboda hazakarsa, inda yake ganin yaki da rashawa ba a baki ake yinsa ba, illa a aikace.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng