Najeriya 2019: Abubuwa 19 da matasan Najeriya ke jira sabuwar gwamnati tayi musu, kowaye kuwa yaci zabe

Najeriya 2019: Abubuwa 19 da matasan Najeriya ke jira sabuwar gwamnati tayi musu, kowaye kuwa yaci zabe

Wannan rubutu dai hange ne da hasashen abubuwan da matasa ke bukata, ra'ayi ne na marubuci Mubarak Bala na Kano, wanda ba lallai ya zama ra'ayin kowanne ma'aikaci a Legit.ng ba. Sakon Tes kawai na iya zuwa 08032880989, kada a kira, sms text kawai).

- Akwai abubuwa da yawa da 'yan Najeriya ke bukata daga shugaban kasa a badi

- Abubuwan zasu kawo gyara da cigaba ga kasa, musamman matasan talakawa

- Ilimi shine jigon cigaban al'umma, sannan tsaron lafiya da dukiya

Najeriya 2019: Abubuwa 19 da matasan Najeriya ke jira sabuwar gwamnati tayi musu, kowaye kuwa yaci zabe
Najeriya 2019: Abubuwa 19 da matasan Najeriya ke jira sabuwar gwamnati tayi musu, kowaye kuwa yaci zabe
Asali: Depositphotos

Gabanin zabe, jiga-jigan 'yan siyasa na manta asalin suwa suke zabe, mata ne, da maza, iyaye da matasa, kwararru da marasa wayau, marasa qarfi da masu karamin karfi, sukan kakaba wa kasar nan abubuwan da su suka hanga, basu damu suji ko mu talakawa me yafi damunmu ba, watakil ma, basu gane me ke damun jama'a ba, saboda sunyi nisa da talakka.

Ga dai kadan daga abubuwan da matasa ke bukata daga kowane ne zai shugabanci kasar Najeriya a 2019 sun hada da:

1. Soke wulakanta yara, dukansu a ciki da wajen makaranta, almajiranci, talla da aikin boyi boyi. Tilasta karatu ga duk yaron da bai kai shekaru 12 ba a duniya.

2. Gina sabbin rukunan dakunan kwana a makarantun gaba da sakandire, 2 na dalibai mata sai daya na maza.

3. Bashin N250,000 ga mata masu sana'ar hannu, N150,000 kuma ga maza.

4. Gina cibiyar kiwon lafiya daya a duk gunduma ta zabe, don saukake haihuwa ga mata da kuma kiwon lafiya.

5. Maida mahukuntan majalisun kasa bai-daya don rage kudin da ake kashewa don biyan su. Ko a soke ta Dattijai ko ta Wakilai.

6. Karancin albashi ya zama N120,000 amma za'a iya sasanta wa.

7. Gina gidaje masu saukin kudi ga ma'aikatan gwamnati tare da bada fili kyauta ga 'yan kasa marasa aikin yi, ko sayarwa suka yi sun rage zafin talauci.

8. Tara kudi asusun ketare ya tsaya a kalla dala biliyan dari $100b. Wannan zai karfafa Naira a gida

DUBA WANNAN: Tunatarwa gareka ya shugaba Buhari: Kan alkawarinka a 2015 na yadda zakayi bayan ka gama da Boko Haram

9. Kawo karshen ta'addancin da sunan addinai, hana yada zafafan aqidu da fadace fadace tsakanin malaman addinai.

10. Tsaro ta fannin abinci: Ka'ida ne a ajje rumbunan abinci fal da abinci a yankunan kasar nan, dongudun ko-ta-baci.

11. Samar da hanyoyin samar da wutar lantarki ta hanyar iska da rana don gujewa yankewar lantarki. Tunda an gaza samar da ta Hydro da ta Gas.

12. Saka matasa a fannin siyasa, mulki da shugabanci, don a dama dasu, kuma su koya.

13. Bari tare da karfafa auratayya tsakanin yaruka, kabilu da addinai mabambanta. Wannan zai batar da tsana ta tsakanin kabilu ko dariqu cikin addinai.

14. Samar da tallafin kudi ga karuwai saboda wadanda ba sha'awa ke kai su ba, sai don neman jari.

15. Samar da aiyuka masu tarin yawa ga 'yan kasa. Ayi koyi da China da Ethiopia.

16. Tsare rayuka da dukiyoyi. Halaka yan ta'addan da suka ki aje makamai, masu garkuwa da mutane, yan fashi da masu tozarta yara.

17. Yada ilimi wanda ba sai a aji ko makaranta ba, wannan ana iyawa ta hanyar shiye-shiryen talabijin, rediyo, wayoyi, majigi da ma 'yan aljannu na zane ko 'yar tsana.

18. A maida kudin tafiyar da gwamnati kadan, kudin ayyuka yafi yawa a kowanne kasafin kudi na kowacce shekara.

19. Wannan an barshi bude, kowa na iya saqala abin da yaso a matsayin cikon na 19.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel