Gwamnatin Buhari za ta kaddamar da fara aikin wasu manyan madatsan ruwa guda 7

Gwamnatin Buhari za ta kaddamar da fara aikin wasu manyan madatsan ruwa guda 7

Ministan ruwa na Najeriya, Injiniya Suleiman damu ya bayyana cewa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta kammala aikin manyan madatsan ruwa guda bakwai a fadin Najeriya, wanda a yanzu haka ana gab da kaddamar da fara aikinsu.

Minister Adamu ya bayyana haka ne a ranar Alhamis 6 ga watan Disamba yayin dayake zayyana cigaban da ma’aikatarsa ta samu cikin shekaru uku da suka gabata, inda yace baya ga madatsan guda bakwai, akwai wasu madatsai guda tara da gwamnatin ta gada, wanda a yanzu haka ta kammala aikinsu, har sun fara aiki.

KU KARANTA: Rundunar Yansandan Najeriya ta bankado shirin kai hare hare da wasu miyagu ke yi a Benuwe

Majiyar Legit.com ta ruwaito daga cikin madatsan ruwan da aka kammala guda bakwai akwai; madatsan ruwa na kashimbila dake Taraba, na Ogwashi-uku dake jahar Delta, na shagari dake jahar Sakkwato, Galma na jahar Kano da Ekeremor na jahar Edo.

Sauran sun hada da madatsan ruwa na Mangu dake jahar Filato da kuma na jami’ar noma ta gwamnatin tarayya dake jahar Benuwe, kamar yadda jaridar Daily trust ta ruwaito ministan ruwa na fadi.

Haka zalika minista Adamu ya bayyana wasu daga cikin madatsan ruwan da aka kammala har ma suka fara aiki sun hada da madatsan ruwa na Ogbia dake jahar Bayelsa, na Ojirami dake jahar Edo, na Sabke, Mashi da Dutse dake jahar Katsina, sai kuma na Takum dake Taraba da na Kargo, da Jaji duka a jahar Kaduna.

Bugu da kari ministan ya bayyana wasu cibiyoyin noma rani guda tara da ake sa kammaluwarsu a nan da shekaru biyu masu zuwa da suka hada da aikin noman rani na Tsakiyar Ogun dale jahar Oyo, Rima dake jahar Sakkwato, Gari ta jahar Kano, Kwantagora dake jahar Neja, Bagwai dake jahar Kano.

Sauran sun hada da Tada Shonga na jahar Kwara, Adani na jahar Anambra, Ekuku na jahar Kogi, Ile Ife na jahar Osun, Zaura da na jahar Kebbi, Otukpo na jahar Benuwe, da na Ogbese Ekiti.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel