An sake kwato 'yan Najeriya 200 daga qangin Bauta a Hamadar Saharar Libya

An sake kwato 'yan Najeriya 200 daga qangin Bauta a Hamadar Saharar Libya

- Hukumar NEMA ta sake amsar gudaddu daga Libya

- Ana ta tsere wa daga Najeriya ne lokacin zafin talauci na 2015-17

- Anyi ta mutuwa a hamada, sannan an bautar da dama

An sake kwato 'yan Najeriya 200 daga qangin Bauta a Hamadar Saharar Libya
An sake kwato 'yan Najeriya 200 daga qangin Bauta a Hamadar Saharar Libya
Asali: UGC

Kokarinn gwamnatin Tarayya na ceto masu kokarin shiga Turai neman sabuwar rayuwa, da ma kuma wadanda tsautsayi yasa aka yaudare su aka tafi dasu don sayarwa ayi karuwanci ko bautarwa yanzu ya sake samo 197 a hamada.

Sun dai galabaita, sannan sun sha wuya, kuma duk guzurinsu ya qare.

Sanin kowa ne yadda matsin tattalin arziki yayi wa jama'a katutu a lokacin hawan mulkin shugaba Buhari, dalili da faduwar farashin mai da ma matse tattalin aljihun gwamnati, a kokarin ta na rage beranci.

Cibiyar taimakon gaggawa, NEMA a ranar Alhamis ta karbi yan Najeriya 193 daga Libya.

Ofishin dillancin labarai ya ruwaito cewa Segun Afolayan, mukaddashin mashiryin NEMA na yankin kudu maso yamma ya tabbatarwa da manema labarai cigaban.

Afolayan yace yan Najeriya sun iso ne da karfe 8:32 na dare a filin jirgin Murtala Muhammed dake Legas.

Yace kungiyar yan gudun hijira ta duniya ce ta taimakawa dawowa dasu karkashin shirin taimakon komawa na kyauta.

Afolayan yace masu dawowar sun hada da mata manya 81,yarinya mace 1 da jarirai mata 14. Akwai maza manya 87,yara maza 5 da jarirai 5 maza. Ya hori yan Najeriya dasu dena nuna kyama ga wadanda suka dawo kasar bayan da suka je kasashen ketare don neman arziki.

Kamar yanda yace, "Damar kowa ce da yayi rayuwar shi babu tsangwama ba amma kuma hanyar samu cikakkiyar dama itace wadatuwar zuciya. Da yawa daga cikin wadanda suka fita kasashen wajen basu san hatsarurrukan dake kan hanyar ba.

Suna fadawa alkawurran makaryata da mayaudara na rayuwa mai inganci a wajen kasar nan. Yakamata yan Najeriya su karbi kalubalen hijira ba bisa ka'ida ba kuma yakamata mu hada karfi da karfe wajen ceto matasan mu dake fadawa wannan harkar. "

Ya shawarci wadanda suka dawo dasu kwantar da hankalin su tare da maida hankali gurin gyara rayuwar su a Najeriya. Kamar yanda yace Gwamnatin tarayya, IOM da kungiyar hadin kan turai suna samar da damammaki ga wadanda suka dawo na koyon sana'a.

Afolayan ya roki yan kasa dasu taimakawa Gwamnatin wajen kara hada kai da wadanda suka dawo don amfanar kansu.

DUBA WANNAN: Nafi karfin maula a hannun 'yan siyasa - Oyedepo ke maida martani bayan katobaras Father Mbaka kan kin sadaqar Peter Obi ga Coci

Miliyoyi ne daga nahiyar Afirka ke tserewa don shiga Turai, kuma da yawa daga Najeriya daga Kudu suke. Sai dai in sun je Libya ana kama su a bautar ko a azabtar.

Wadanda aka ceto a wannan karon sun sauka daga jirgi a Legas, inda hukumar NEMA tta amshe su saboda a tantance lafiyarsu da bukatunsu na gaggawa, sannan a mika su izuwa yankunan da suka fito.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel