'Tsofi da suka haura 70 su hakura da takara su bar wa yara masu jini a jika'

'Tsofi da suka haura 70 su hakura da takara su bar wa yara masu jini a jika'

- Yakamata duk wani dan siyasa da yayi shekaru 70 ya hakura ya barwa matasa

- Idan kuma suna tunanin har yanzu sunada karfin da zasu iya mulki to su sanya kishin kasa a zukatansu

- Tsohon Shugaban soja Abdulsalami Abubakar ne yayi wannan shawara

'Tsofi da suka haura 70 su hakura da takara su bar wa yara masu jini a jika'
'Tsofi da suka haura 70 su hakura da takara su bar wa yara masu jini a jika'
Asali: UGC

Duk wani dan siyasa da yasan yayi shekaru 70 ya kamata ya hakura haka yabarwa matasa kuma, fadin tsohon Janar Abdussalami a Kaduna, a wani shagube da ake sa rai yana yi wa Janar ne Muhammadu Buhari, wanda shaqiqansa Obasanjo da IBB suka juyawa baya a bana.

Sai dai kuma, dan takara da ake sa rai suna mara wa baya, duk da dattijon baya siyasa a fili, Atiku Abubakar, shima ya haura 70 din.

Tsohon Shugaban soja Abdulsalami Abubakar ne ya bada wannan shawara a Arewa House dake jihar Kaduna a yayin kaddamar da wani littafi mai suna "Yakowa: A dream differed".

Ya kara da cewa idan kuma suna tunanin suna da karfin da zasu iyayin shugaban cin to su sanya kishi a cikin zukatansu dan samawa kasar zaman lafiya da kwanciyar hankali.

DUBA WANNAN: Aikin Oshiomhole ya sake dawowa baya, lokacin da tsohon shugaban APC Oyegun ke neman dawowa kujerarsa

Tsohon gwamnan jihar yace "yan siyasar dake tunanin suna da karfin mulkar kasar to su sanya kishi ta haka ne zasu samu damar saisaita kasar".

"Ina shawartarku dakuyi camfe a bisa abubuwan da suka kamata,Y 'an siyasa da jam'iyun su su rike wani abu wanda zai samarwa da kasar kwanciyar hankalinmu kuma zamuci gaba da basu shawara akan abinda ya kamata har zuwa lokacin da kasar zata zama mai inganci."

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel