Masoya Buhari sunce zasu saya ma Atiku tikitin zuwa ziyara Amurka

Masoya Buhari sunce zasu saya ma Atiku tikitin zuwa ziyara Amurka

- Wata kungiyar goyon bayan Buhari tayi alkawarin samarwa Atiku Abubakar tikitin jirgi don zuwa Amurka

- Wannan ya biyo bayan ikirarin da PDP keyi na cewa Amurka ta ba Atiku tikitin shiga kasar

- Kungiyar ta san Atiku na da kudin siyan tikiti har ma quri'a

Masoya Buhari sunce zasu saya ma Atiku tikitin zuwa ziyara Amurka

Masoya Buhari sunce zasu saya ma Atiku tikitin zuwa ziyara Amurka
Source: Facebook

Kungiyar goyon bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari wacce aka fi sani da NATBuhariOsinbajo 2019 sunyi alkawarin samarwa dan takarar shugabancin kasa karkashin jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, tikitin jirgi na ajin farko a kowanne kamfanin jirgin sama wanda yake ra'ayi domin fitar da zargin da yan Najeriya keyi mishi na cewa bashi da damar shiga Amurka.

Wannan ya biyo bayan maganar PDP na cewa kasar Amurka ta ba wa Atiku tikitin shiga kasar.

Atikun, anjiyo shine yana neman bizar zuwa Amurka, duk da dai ga alama hakan bai yiwu ba, lamari da bai yi wa yan jam'iyyarsa dadi ba.

DUBA WANNAN: Hadimin gwamna ya bar kujerarsa ya sauya jam'iyya

Gwamnati ma ta gargadi gwamnatin Amurka da kada ta kuskura ta baiwa Atiku bizar zuwa kasarta, wai don a baya ana zarginsa da aikata laifukan yawo da makudan kudi a kasar, kan wata kwangilar gwamnati.

Shugaban kungiyar ta kasa, Vincent Ubah, yace: "Wannan tayin ba yana nuna cewa kungiyar bata san cewa Atiku na da arzikin siyan kuri'u ba ma a ranar zabe. Duk da haka wannan tayin ya zama dole ne don ganar da yan kasa cewa wadanda ke karkashin bincike basu samu damar zama a manyan tarukan duniya ba a matsayin shugaban kasar Najeriya inda kuwa za a iya kama shi a kowanne lokaci."

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel