Kotu tasa EFCC ta kamo mata dan takarar gwamna a APC ta jihar Taraba

Kotu tasa EFCC ta kamo mata dan takarar gwamna a APC ta jihar Taraba

- Kotu ta bawa EFCC umarnin kama dan takarar gwamna a jam'iyar APC

- Ana tuhumar sa da karbar kudi daga wajen tsohon shugaban kasa Goodluck

- Kotun ta nemi EFCC data gurfanar da Sani Abubakar a ranar 15 ga watan Junairu

Kamfanin giya ya kai agaji makarantun jihar shari'a ta Kano, sun kuwa amsa

Kamfanin giya ya kai agaji makarantun jihar shari'a ta Kano, sun kuwa amsa
Source: Depositphotos

A ranar Laraba wata babbar kotu dake zaman ta a Jalingo ta bawa EFCC umarnin kama dan takarar gwamna a jam'iyar APC.

Ana zargin tsohon Dan takarar gwamna a jihar Taraba Alh.Sani Danladi tare da wasu mutane biyu da karbar kudi wanda yawan su yakai naira miliyan 450.

Ana zargin sun karbi wannan kudi ne daga hannun tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan a lokacin zaben shekara ta 2015 a jihar.

DUBA WANNAN:Jaridar Economist: Buhari zai zarce a badi, Ta'addanci zai ci gaba a Najeriya Bangaren Atiku: Wannan soki burutsu ne

Mai shari'a Steven Pam ya bada umarnin ne bayan yaji daga bakin wadanda ake zargin su Uku.

Kotun ta umarci EFCC data gurfanar da dan takarar gwamna a jam'iyar APC Alh.Sani Abubakar Danladi a gaban ta a ranar 15 ga watan Junairu.

A bangare daya kuma a wajen kotun taron matasa ne dauke da allo suna rokon gwamnati ta hannun hukumar ta EFCC da ta rabu da Danladi zai bayyana a gabanta da kanshi.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel