Buharin da mu ka sani ne wannan ba Jibril daga Sudan ba Osita Chidoka

Buharin da mu ka sani ne wannan ba Jibril daga Sudan ba Osita Chidoka

- Kwamitin yakin neman zaben Atiku yayi magana game da batun Jibril daga Sudan

- Osita Chidoka yace babu burbushin gaskiya a cewa an kirkiri mai kama da Buhari

- Mai magana da yawun na Atiku ya nemi a rika fadawa jama’a gaskiyar halin Buhari

Buharin da mu ka sani ne wannan ba Jibril daga Sudan ba Osita Chidoka

Atiku yace Buharin da ake gani shi ne na asali ba wani mutumi ne daga Sudan ba
Source: Depositphotos

Mun samu labari cewa ‘Dan takarar Shugaban Kasa a Jam’iyyar adawa ta PDP, Atiku Abubakar ya tofa albarkacin bakin sa da maganar da ake yi na cewa an kirkiro wani mai kama da Shugaban kasa Muhammadu Buhari daga Sudan.

Atiku ya karyata rade-radin cewa fadar Shugaban kasa tayi hayar wani mutumi ne mai suna Jibril Aminu Al-Sudani inda yace yadda Shugaba Buhari ya rika boyewa ‘Yan Najeriya ainihin halin da yake ciki ya jawo wadannan ka-ce-na-ce.

KU KARANTA: Ana shiryawa Shugaba Buhari wani mugun tuggu - Inji Osinbajo

Osita Chidoka, wanda yana cikin Darektocin kwamitin yakin neman zaben Atiku Abubakar ya bayyana wannan a lokacin da yayi wani jawabi a gidan Talabijin na AIT. Chidoka ya nemi a rika fayyacewa jama’a gaskiyar rashin lafiyar Shugaba Buhari.

Chidoka yayi tir da yadda aka rike boyewa jama’a rashin lafiyar Shugaban kasar a wancan lokaci. Ya kuma ce har yanzu babu wanda ya san cutar da Shugaban kasar yayi fama da ita ko kuma adadin kudin da aka kashe ko Likitocin da su ka duba sa.

Jiya kun ji cewa Ministan harkokin waje na Najeriya, Mista Geoffrey Onyeama ya bayyana cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai amince da duk yadda sakamakon zaben 2019 ya kama a Najeriya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel