Yajin aiki: An kasa cimma matsaya a tattaunawa tsakanin gwamnati da kungiyar Malamai

Yajin aiki: An kasa cimma matsaya a tattaunawa tsakanin gwamnati da kungiyar Malamai

An tashi baram baram ba tare da cimma matsaya ba a zaman tattaunawa daya gudana tsakanin kungiyar Malaman jami’o’in Najeriya, ASUU, da gwamnatin Najeriya akan yajin aiki na dindindin da ASUU ta shiga tun kimanin wata daya daya shude.

Majiyar Legit.com ta ruwaito an gudanar da wannan zama ne a ranar Talata 4 ga watan Disamba a ofishin ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu, wanda ya gayyaci yayan kungiyar ASUU don tattauna hanyoyin shawo kan matsalolin da suke fama dasu.

KU KARANTA: Yansanda sun kama wata Mata da ta jefar da jaririnta a Gombe

Dayake ganawa da manema labaru, shugaban ASUU, Biodun Ogunyemi ya bayyana cewa har yanzu basu cimma matsaya ba a tattaunawa da suke yi da gwamnati, inda yace ana nan ana ta jayayya da yi ma juna tayi.

“Zuwa yanzu dai mun fara tattaunawa, amma dai bamu cimma wata takamaimen matsaya ba, idan harm un samu wasu muhimman bayanai, zamu bayyana ma manema labaru, kungiyarmu zata koma ta zauna da yayanta.” Inji shi.

A ranar 4 ga watan Nuwamba ne ASUU ta shiga yajin aikin dindindin saboda karancin kudaden da gwamnati take baiwa jami’o’in Najeriya da kuma zargin da tayi ma gwamnati na kin cika alkawarin data dauka na aiwatar da yarjejeniyar da ta cimmawa da ASUU a shkarar 2009.

Sai dai a hannu guda kuma, shugaban kungiyar daliban Najeriya, Danielson Akpan ya bayyana damuwarsa da yadda gwamnati da ASUU suka gagara cimma matsaya a tsakaninsu, inda yace ya kamata su tausaya ma dalibai su sulhunta kansu.

“Ya kamata bangarorin biyu su sanya bukatar Najeriya da maslahar dalibai a sama fiye da muradunsu, don haka muke kira dasu daure su sulhunta kansu ko dalibai zasu samu damar komawa makaranta domin cigaba da karatu.” Inji Akpan.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel