Yadda Saraki ya ci amanar mu a kan biyan bukatar sa - Tinubu

Yadda Saraki ya ci amanar mu a kan biyan bukatar sa - Tinubu

- Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya yi kaca-kaca da shugaban majalisa Bukola Saraki da Atiku Abubakar

- Jagoran jam'iyyar APC na kasa ya kallubalanci Atiku Abubakar ya fito ya yi bayani a kan baddakalar Halliburton

- Bola Tinubu kuma ya ce Bukola Saraki ya ci amanar jam'iyyar APC saboda ya biya bukatun kansa

Jagoran jam'iyyar APC na kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya kallubalanci dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar a kan baddakallar cin hanci na kamfanin Halliburton.

Tsawon shekaru, Hukumar yaki da masu yiwa arzikin kasa ta'annati EFCC ta dade tana bincike a kan kamfanin kasar Amurka wato Halliburtan kan zargin bayar da cin hanci na zunzurutun kudi sama da $182 miliyan kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Tinubu ya kalubanci Atiku a kan badakalar Haliburton, ya ce Saraki ba shi da gaskiya

Tinubu ya kalubanci Atiku a kan badakalar Haliburton, ya ce Saraki ba shi da gaskiya
Source: Depositphotos

A jawabin da ya yi wajen taron kasa da kwamitin kungiyoyi masu goyon Buhari na kasa suka shirya, Tinubu ya ce ba zai yiwu 'yan Najeriya su koma kangin bauta ba bayan an ceto su daga wadanda ke zaluntarsu.

DUBA WANNAN: A bamu makamai mu yaki 'yan ta'adda - Babban Sarki a Zamfara ya roki Buhari

"Sun ce mu dena magana kan abubuwan da suka wuce. Dole ne mu duba abinda ku kayi a baya. Zamu duba batun Halliburton. Mene yasa ta fice daga Najeriya? An kashe Dallan Amurka Biliyan 16 a NEPA amma har yanzu wasu na cikin duhu...

"Yayin da suka lura za mu kwace mulki daga hannunsu, sun garzaya sun sayarwa 'yan kasuwan kamfanoni, amma ni ganinsa na ke kawai sun raba wa junansu dukiyar 'yan Najeriya ne," inji shi.

A yayin da ya yi tsokaci a kan shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, Tinubu ya ce bayan ya yi amfani da APC ya lashe zabe a 2015, "Saraki ya yi amfani da kason da muka bashi domin karfafa PDP. Hali nagari yana da muhimmanci a shugabanci. Ya fice daga PDP, ya shigo APC, bayan ya lashe zabe sai ya sayar da kason da muka bashi saboda bukatar kansa. Allah mai gaskiya ne amma Saraki bashi da gaskiya."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel