Sabuwar kimiyya zata rage yawan barin ciki da mutuwar jarirai a ciki

Sabuwar kimiyya zata rage yawan barin ciki da mutuwar jarirai a ciki

- Masana kimiyya sun samar da wata karamar mahaifa

- Wannan karamar mahaifa zata taimaka wajen hana yin bari da kuma macewar yaro ciki

- Mafi yawan matsalolin ciki suna faruwa ne a watanni ukun farko na samuwar cikin

Sabuwar kimiyya zata rage yawan barin ciki da mutuwar jarirai a ciki
Sabuwar kimiyya zata rage yawan barin ciki da mutuwar jarirai a ciki
Asali: Depositphotos

Masana kimiyya sun kirkiri wata karamar mahaifa wadda zata taimakawa matan dake fama da matsalar haihuwar matacce, bakwaini da kuma masuyin girgiza a yayin haihuwa.

Duk wadannan matsaloli suna farawa ne a watanni Uku da samuwar ciki wanda a wannan lokaci masana basa iya ganin abunda yake faruwa a cikin mace.

Wannan kungiya wadda jami'ar Cambridge ta jagoranta sun samar da wannan karamar mahaifa ne wadda ta kasance ido baya iya ganin ta amma zata taimaka wajen yiwa masu ciki gwaje gwaje.

DUBA WANNAN: Jam'iyyu basu so ayi aiki da sabuwar dokar zabe

Muna fata nan gaba wannan mahaifa zata taimaka mana wajen gano dalilin dayasa wasu matan ke shan wahala idan sun samu ciki. Cewar wani farfesa a jami'ar ta Cambridge.

Masanan sun ce wannan kwaya ta karamar mahaifa zata bada damar sanin meyasa kananun kwayoyin cuta musamman Zika suke shiga cikin mahaifa su cutar da jaririn dake ciki.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel