A bamu makamai mu yaki 'yan ta'adda - Babban Sarki a Zamfara ya roki Buhari

A bamu makamai mu yaki 'yan ta'adda - Babban Sarki a Zamfara ya roki Buhari

Sarkin Anka kuma Ciyaman din Sarakunan jihar Zamfara, Alhaji Attahiru Muhammad Ahmad ya roki gwamnatin tarayya ta samar musu da bindigu wadda za suyi amfani da shi domin tunkarar 'yan bindiga da ke kashe-kashe da garkuwa da mutane a sassan jihar.

Sarkin ya yi wannan jawabin ne a yayin da ake rabawa sabbin 'yan bangan sa kai na Civilian JTF babura 850 a jihar.

Ya ce 'yan bindigan da ke garkuwa da mutane da kashe-kashe suna amfani da sabbin bindigan irinsu AK 47 ne wajen kaiwa mutane hari saboda haka ya dace suma a bawa mutanensu irin wannan makaman domin su tunkari 'yan bindigan ba tare da wani fargaba ba.

A bamu makamai mu yaki 'yan bindiga - Sarkin Zamfara ya roki Buhari
A bamu makamai mu yaki 'yan bindiga - Sarkin Zamfara ya roki Buhari
Asali: Twitter

"Muna cikin babban matsala, abubuwa suna kara tabarbarewa a kullum. 'Yan bindigan sun canja dabara saboda haka ya zama dole hukumomin tsaro suma su canja dabara. Ya kamata a baza jami'an tsaro a wuraren da aka saba kai hari," inji shi.

DUBA WANNAN: Ba zan sake korafi a kan matsalolin Najeriya ba - Buhari

Basaraken ya yi bayanin cewa al'ummar jihar suna cikin bala'i duk da cewa an karo yawan jami'an tsaro a jihar saboda har yanzu hare-haren da 'yan bindigan ke kaiwa bai ragu ba.

Sarkin ya kuma roki mutanen jihar su dena biyan kudin fansa idan anyi garkuwa da 'yan uwansu inda ya ce idan an kashe dan uwansu ya yi jihadi ne.

A jawabinsa, Kwamishinan kananan hukumomi da harkokin sarauta, Alhaji Bello Damkande Gamji ya ce kudin tsarin mulkin Najeriya ya fayyace wadanda ya kamata su rike makamai kuma ya mika godiyarsa da gudunmawar da sarakunan gargajiya ke bayarwa wajen tabbatar da zaman lafiya a jihar.

Ya ce sun gano cewa duk adadin hukumomi tsaro da za a kawo jihar ba zai warware matsalar ba shi yasa su kayi hadin gwiwa da 'yan sintirin sa kai wato Civilian JTF saboda sune suka san lungu da sakunnan da ke garin kuma za su taimaka wa hukumomin tsaro sosai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel