Tsohon gwamnan PDP ya musanta mallakar manyan kadarori da EFCC ta bankado a Kaduna
- Tsohon gwamnan jihar Filato, Jonah Jang, ya ce ba zai amsa gayyatar EFCC ba saboda bashi da bayanin da zai bayar
- A wani jawabi da gwamnan ya fitar, ya musanta mallakar gidan miliyan N500m da EFCC ta bankado a Kaduna
- Tsohon gwamnan ya bukaci magoya bayansa su dage da addu'o'i, tare da bayyana cewar maganar gayyatar da EFCC ke yi masa na gaban kotu
Tsohon gwamnan jihar Filato, Jonah Jang, ya ci al washin cewar ba zai amsa gayyatar hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arziki (EFCC) ba bisa zargin cewar ya mallaki wasu manyan gidaje na miliyan N500m a garin Kaduna.
A wani rubutaccen jawabi ya aikewa jaridar The Punch, Jang ya musanta batun mallakar gidajen tare da kalubalantar EFCC ta tabbatar da cewar gidajen mallakar sa ne.
A wata sanarwa da EFCC ta fitar jiya, Lahadi, ta ce ta gano gidaje guda biyu mallakar Jang da ke fuloti mai lamba 8 da 9 a unguwar Rimi GRA da ke cikin garin Kaduna.
Tony Orilade, mukaddashin kakakin hukumar EFCC ta ce binciken binciken da su ka gudanar ya nuna ma su cewar an sayi kadarorin ta hanyar amfani da wani kamfani suna Nigerian Development Company (NNDC) da ke Kaduna.
Ya kara da cewar tun a ranar 7 ga watan Mayu, 2018, EFCC ta gurfanar da tsohon gwamnan bisa zarginsa da badakalar kudin da yawansu ya kai N6.3bn.
DUBA WANNAN: Jirgin kasa ya mirtsike wani matsahi a Abuja
Jang, sanata mai wakiltar jihar Filato ta tsakiya a majalisar dattijai ta kasa, na fuskantar tuhumar almundahana da almubazzaranci da dukiyar jama'ar Filato da jihar ta karba daga babban bankin kasa (CBN) lokacin yana gwamna.
EFCC ta ce ce tsohon gwamnan ya tafka almundahana da kudin jihar Filato da yawansu ya kai N4.3bn ta hanyar amfani da sakataren gwamnatinsa, Yusuf Pam.
Daya daga cikin tuhumar da ake yiwa gwamnan ta nuna yadda ya karkatar da N2bn kudin tallafin ma su matsakaita da kananun masana'antu da CBN ta bawa jihar sa kafin karewar wa'adinsa a watan Afrilu na shekarar 2015.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng