Cikin shekaru biyu: A Kaduna kadai a arewa, mutum N700,000 ne suka sami agaji da bayanai a cutar HIV

Cikin shekaru biyu: A Kaduna kadai a arewa, mutum N700,000 ne suka sami agaji da bayanai a cutar HIV

- UNICEF ta tallafawa matasa sama da 700,000 wadanda ke dauke da cutar HIV

- Hukumar ta samu wannan nasara ne a cikin shekaru Biyu

- A halin yanzu mutane 90,000 dake dauke da wannan cuta tayi kasa a jikin su

Cikin shekaru biyu: A Kaduna kadai a arewa, mutum N700,000 ne suka sami agaji da bayanai a cutar HIV
Cikin shekaru biyu: A Kaduna kadai a arewa, mutum N700,000 ne suka sami agaji da bayanai a cutar HIV
Asali: Depositphotos

UNICEF sashen jihar Kaduna tace sun samu nasarar taimakawa matasa 700,000 wadanda ke dauke da cutar HIV a cikin shekaru biyu.

Dr Idris Baba wanda ya kasance kwarraren likitan hukumar ya bayyana haka ne a Kaduna a ranar Asabar a yayin da ake gudanar da taron ranar AIDS na duniya.

Baba yace sunyi hadin gwiwa ne da jihar Kaduna a sanda suka fara gudanar da wannan shiri a kananan hukumomi bakwai dake jihar.

DUBA WANNAN: Yadda yara suka kashe Mamman Nur na Boko Haram

Ya bayyana kananan hukumomin wadanda suka hada da Jaba, birnin Gwari, Jama'a, Jere, Kagarko, Igabi da kuma Chikun.

A halin yanzu mutane 90,000 daga ciki an samu cutar tayi kasa a jikinsu.

Jihar Kaduna dai ana kiranta da bariki, inda matasa maza da mata, daga kowanne sashe na yankin arewacin kasar nan kanzo don hutawa, sheqe aya ko neman'yanci. Sai dai wannan na zuwa da rashin ilimi, da fahimtar kiwon lafiya.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel