Jihohi uku da suka fi kowacce tara kudi a bana, da uku na can qarshe a iya karbar haraji

Jihohi uku da suka fi kowacce tara kudi a bana, da uku na can qarshe a iya karbar haraji

- Bincike ya bayyana jihohin da suka karbi haraji mafi tsoka a cikin atanni shida na 2018

- Gwamnatin Najeriya na son ta yaye jihohi amma sunqi girma

- Jihar Legas ita ce tafi kowacce samun kudaden shiga

Jihohi uku da suka fi kowacce tara kudi a bana, da uku na can qarshe a iya karbar haraji
Jihohi uku da suka fi kowacce tara kudi a bana, da uku na can qarshe a iya karbar haraji
Asali: Depositphotos

Rahoton hukumar kudiddiga da aka fitar ya bayyana jerin jihohin da suka samu suka iya tara maqudan kudade a bangaren haraji da suke karba a cikin watanni shida na shekara ta 2018.

Dama dai ya kamata kowacce jiha ta iya sama wa kanta kudade, maimakon wai ace sai gwamnatin Tarayya ta aiko sannan za'a yi albashi da ayyuka.

Shekaru kusan 30 da kirkirar jihohin, amma har yanzu gwamnatin Tarayya ke basu nono, ta kasa yaye su, su kuma sun zame wa Najeriya nauyi.

DUBA WANNAN: Auren Priyanka ya lakume N21b

Rahoton ya kuma bayyana jihohin da suka karbi haraji mafi kankanta duk a cikin watanni shida na shekara ta 2018.

Rahoton ya bayyana cewa jihar Legas itace jihar data karbi haraji mafi tsoka a cikin jerin wadannan jihohi.

Ga yadda rahoton ya bayyana:

Jihohin da suka karbi haraji mai tsoka

- Jihar Legas N196b

- Rivers N60.9b

- Ogun N42.5b

Jihohin da suka tara haraji mafi karanci

- Jihar Gombe N2.3b.

- Jihar Kebbi N2b

- Jihar Yobe N1.6b

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel