'Yan sanda sun yi karin haske a kan bayyanar wasu bakin 'yan bindiga a Sokoto

'Yan sanda sun yi karin haske a kan bayyanar wasu bakin 'yan bindiga a Sokoto

- Hukumar yan sanda ta ce mutanen aka ce an gani a karamar hukumar Tangaza na jihar Sokoto ba a Najeriya suke ba

- 'Yan sandan sun ce Tangaza yana kan iyakar Najeriya da jamhuriyar Nijar ne shi yasa ake ganin mutanen suna harkokinsu

- Hukumar 'yan sanda tayi kira da al'umma sun kwantar da hankulansu duk da cewa ta ce za ta baza jami'anta domin ganin mutanen ba su shigo Najeriya ba

Hukumar 'yan sanda reshen jihar Sokoto ta ce 'yan sabuwar kungiyar da aka ce an gani a wani bangare na jihar ba mazauna Najeriya bane kuma ba su dauke da bindigu kamar yadda akayi ikirari da farko.

A baya, Premium Times ta ruwaito cewa wasu mazauna karamar hukumar Tangaza sunyi korafin cewa wasu 'yan kungiya sun shigo sassan karamar hukumar Tangaza dauke da makamai suna karbar zakka daga hannun mutane.

Sai dai, Hukumar 'yan sandan ta bayyana cewa lamarin ba haka yake ba.

'Yan sanda sun yi karin haske a kan bayyanar wasu bakin 'yan bindiga a Sokoto
'Yan sanda sun yi karin haske a kan bayyanar wasu bakin 'yan bindiga a Sokoto
Asali: Twitter

A sanarwar da ta fitar ranar Juma'a, kakakin 'yan sandan jihar, Cordelia Nwawe ta shaidawa majiyar Legit.ng cewa kwamishinan 'yan sanda, Murtala Mani da mataimakinsa, Baba Isa sun tafi garin Tangaza a ranar Juma'a domin gano abinda ke faruwa.

DUBA WANNAN: Wata sabuwar kungiyar 'yan ta'adda ta kwace iko a karamar hukuma a Sokoto

"Babu wasu 'yan bindiga, mutane su kwantar da hankulansu. Kwamishinan 'yan sanda ta mataimakinsa sun tafi garin sun warware matsalar," inji Mrs Nwawe.

"Babu bukatar mutane su tayar da hankalinsu domin babu ruwan Najeriya da abubuwan da ke faruwa a jamhuriyar Nijar. Mutanen da aka gani mazauna Nijar ne kuma ba dukkan harkokinsu a Nijar su keyi. Tangaza gari ne da ke kan iyakan Najeriya da Nijar, duk da cewa mutane sunyi ikirarin sun ga wasu mutane da rakuma, jakuna da matansu amma ba cikin Najeriya bane.

"Sai dai duk da haka ba zamu nade hannu muna kallo ba, mun aike da jami'an mu zuwa garin domin su tabbatar 'yan kungiyar ba su shigo Najeriya ba," inji Mrs Nwawe.

Ta ce jami'an 'yan sanda suna gudanar da ayyukansu yadda ya kamata amma ba za su iya shiga Nijar su kamo masu laifi ba.

"Idan wani ya aikata laifi ya gudu Nijar, za mu tuntubi jami'an tsaro na kasar su dawo mana dashi musamman idan a Najeriya aka aikata laifin," inji kakakin 'yan sandan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel