Wata sabuwar kungiyar 'yan ta'adda ta kwace iko a karamar hukuma a Sokoto

Wata sabuwar kungiyar 'yan ta'adda ta kwace iko a karamar hukuma a Sokoto

Rahotanni da muka samu sunyi ikirarin cewa wata sabuwar kungiyar 'yan ta'adda masu dauke da muggan makamai sun kwace iko a karamar hukumar Tangaza da ke jihar Sokoto inda aka ce sun kafa dokokinsu kuma sun ce yankin ta zama ta su.

Premium Times ta ruwaito cewa wani shaidan ido ya ce bisa ga dukkan alamu 'yan kungiyar daga jamhuriyar Nijar su ke. Shaidan ya yi ikirarin cewa 'yan kungiyar na dauke da miyagun makamai kuma suna ikirarin wa'azin addinin musulunci kuma suna tilastawa mutane bayar da zakka.

A cewar rahoton, ana yiwa wadanda suka gaza biyan zakkan bulala.

Rahoton ya ce har yanzu ba a gano sunan 'yan kungiyar amma sun kwashe kimanin watanni biyu a karamar hukumar.

Wata sabuwar kungiyar 'yan ta'adda ta kwace iko a karamar hukuma a Sokoto

Wata sabuwar kungiyar 'yan ta'adda ta kwace iko a karamar hukuma a Sokoto
Source: Twitter

Shaidan ya ce 'yan kungiyar sun horas da matasa a wani daji sannan daga bisani suka raba musu babura.

DUBA WANNAN: Muhimman abubuwa 7 da Buhari ya fadi a Maiduguri

Shaidan ya ce adadin yan kungiyar sun kai kimanin 200 kuma suna da wata irin kammani wadda ba saba gani ba sannan suna magana da larabci kuma suna da rawani a kawunnansu, inji rahoton.

"Sun tilastawa kowanne gida da ke da shanu ko raguna haraji. Masu shanu suna biyan N500 yayin da masu raguna kuma suna biyan N200.

"Suna kama duk wani makiyayi da ya shigo kiwo a gonaki, sannan su ci su tara kuma su rike kudaden.

"Suna cin karensu babu babbaka, sun firgita mutane kuma babu wanda ke kallubalantarsu. Suna zuwa daga unguwa zuwa unguwa," inji shaidan.

Rahoton ya ce kwamishinan yan sandan jihar Sokoto, Murtala Mani yana kan hanyarsa na zuwa karamar hukumar a yayin da aka tuntube shi.

An ruwaito cewar ya ce zai bayar da ba'asi idan ya dawo.

Rahotanni sun ce mai magana da yawun gwamnatin jihar, Abubakar Shekara ya tabbatar da lamarin amma bai bayar da cikaken bayani ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel